Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Spartak Moscow na zawarcin Moyes, Watakila Man Utd ta fasa sayar da Rashford
Manchester United ba ta tsammanin wani kulob zai iya biyan fam miliyan 70 kan ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford dan shekara 26, a bazara . (ESPN)
Paris St-Germain ta dakatar da zawarcin da ta ke yi wa Rashford kuma a yanzu za ta maida hankali akan wasu ‘yan wasan. (iSport)
A wani labarin kuma kocin Man Utd Erik ten Hag ,mai 54, bai sani ba ko zai ci gaba da jagoranci Old Trafford a kakar wasa mai zuwa . (HITC)
Arsenal ta yi wa dan tsakiyar Italiya Jorginho tayin sabon kwantiragi , wanda kwantaraginsa zai zo karshe a watan Yuni ,kuma ana sa ran dan wasan mai shekara 32 zai rattaba hannu. (Athletic - subscription required)
West Ham za ta fuskani hamayya daga AC Milan a kan kocin Lille, Paulo Fonseca, mai shekara 51 a matsayin wanda zai maye gurbin kocin Hammers David Moyes. (i Sport)
Moyes dan yankin Scotland mai shekara 61 ya ja hankalin Spartak Moscow sakamakon rashin tabbas game da makomarsa a West Ham. (Mail)
Dan wasan gaban Chelsea da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 29, be tattauna da wakilan Saudi Pro League game da komawarsa can ba a musayyar bazara, ko da yake Chelsea za ta so ta sayar musu da dan wasa mai kai hari na Belguim Romelu Lukaku, mai shekara 30. (Caughtoffside)
Dan wasan tsakiya na Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 29, ya nuna alamun zai yi nazari game da makomarsa a Manchester United bayan Euro 2024,sai dai a yanzu zai maida hankali a wasan karshe na FA Cup final da kuma gasar da za a yi a Jamus a bazara. (Danz Portugal - in Portuguese)
Kungiyoyi da dama a Saudiyya na zawarcin dan wasan gaban Barcelona da Sifaniya Ansu Fati dan shekara 21 wanda a halin yanzu aka bada shi aro ga Brighton, da kuma tsohon mai tsaron bayan Faransa Clement Lenglet, mai shekara 28, wanda aka ba da shi aro ga Aston Villa. (Sport - in Spanish)
Kawo yanzu Manchester United na son ta cefanar da dan wasan gaban Ingila Mason Greenwood, dan shekara 22, a wannan bazara , kuma za ta yanke shawara a karshen kakar wasani. (Fabrizio Romano)
Chelsea ta musanta cewa ta biya kudin jirgin saman Ruben Amorim zuwa Landan a makon daya gabata ko kuma sun gana da kocin Sporting Lisbon mai shekara 39. (Matt Law, Telegraph, via X)
Borussia Dortmund na son Ian Maatsen ya ci gaba da taka leda a kulob din har bayan kakar wasani bayan da dan wasan gefe na kasar Netherlands dan shekara 22 ya nuna kwazo sosai bayan da Chelsea ta bayar da shi aro (Fabrizio Romano)
Leicester ta tattauna da dan wasa Ingila mai kai hari Jamie Vardu mai shekara 37 gameda tsawaita kwantarigansa a kungiyar . (Mail)
Watakila Crystal Palace ta sayar da dan wasan yankin Ireland a tawagar masu shekaru yan kasa da 21 Killian Phillips, mai shekara 22, a kasuwar cefanar da 'yan wasa ta bazara . (Teamtalk)
Dan wasan tsakiya na Ingila Callum O'Hare, mai shekara 25, wanda Aston Villa da West Ham ke zawarcinsa ya fadawa , Coventry City cewa zai bar kungiyar a wannan bazara . (Football Insider)