Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ci tarar Fulham £75,000 ba za ta sayi matasan ƴan kwallo ba
Mahukuntan Premier League sun ci tarar Fulham £75,000 an kuma dakatar da ita wata shida daga daukar matasan ƴan wasa.
Kenan ba dama ta yi rijistar matasan ƴan wasanta da suke makarantar horon kungiyar ko kuma dauko wasu daga wasu wajen.
Hukuncin ya kunshi wani biyan kudi da kungiyar Cottage ta yi wa Balham Blazers FC da ta kai Fabio Carvalho ya koma Liverpool.
Cavalho, mai buga gurbin cin kwallaye ya koma Fulham daga Balham Blazers a Disambar 2014.
Premier League ta ce Fulham ta amince da cewar ta karya dokar da ta shafi daukar matasa ta hukumar.
An jingine hukuncin daga shekara daya, kenan ya fara aiki daga 15 ga watan Afirilun 2024.
Fulham tana ta 12 a kan teburin Premier League, bayan cin wasa 12 da canjaras bakwai aka doke ta wasa 16.
Haka kuma kungiyar Craven Cottage ta zura kwallo 51 a bana an zura mata 55 a babbar gasar tamaula ta Ingila.