Abu 10 kan Jami'ar ABU da ta cika shekara 60 da kafuwa

An wallafa

Jami'ar Ahmadu Bello Zariya da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya, jami'ar gwamnatin tarayya ce wadda aka kafa ranar 4 ga watan Oktoban 1962. Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ne ya kafa ta, daga nan kuma jami'ar ta ci sunansa.

An kafa mashahuriyar jami'ar ne shekara ɗaya da Jami'ar Obafemi Awolowo ta Ile-Ife da Jami'ar Lagos, a kudancin Najeriya. Ita ce jami'ar farko da aka buɗe a arewacin Najeriya. Albarkacin cikarta shekara 60 da kafuwa, mun tsakuro wasu abubuwa guda goma da muke tunanin za ku so ku sani game da Jami'ar Ahmadu Bello

1. Tsarin ABU Jami'ar Ahmadu Bello Zariya tana da harabobi guda biyu, babbar harabarta tana Samaru da kuma wata Kongo cikin birnin Zariya a jihar Kaduna. Tana kuma da Cibiyar Share Fagen Shiga Jami'a a Funtua cikin jihar Katsina.

A Samaru ne, ginin gudanarwar jami'ar yake kuma tana da tsangayoyin kimiyya da kimiyyar zamantakewa da fasaha da ilmi da tsara muhalli da injiniyaci da kimiyyar likitanci da kimiyyar noma da cibiyoyin bincike suke.

Harabar Kongo kuma akwai tsangayar shari'ah da nazarin gudanarwa, a cewar shafin The Abusite.

Majalisar Dokokin Arewa ta zartar da dokar kafa jami'ar ne a 1961, inda aka haɗe gine-ginen tsangayoyin Kwalejin Fasaha da Kimiyya da Kere-kere ta Najeriya da ke Samaru da Kwalejin nazarin Larabci da Addinin Musulunci ta Ahmadu Bello ta Kano da Cibiyar Bincike kan Harkokin Noma ta Samaru da Cibiyar harkokin Gudanarwa ta Zaria da Cibiyar Bincike kan Likitanci Dabbobi ta Vom a Filato.

Bugu da kari, jami'ar ce ke da alhakin tafiyar da sauran cibiyoyi da shirye-shiryen ilmi daban-daban a sauran wurare.

2. Maƙasudin kafa ABU Tana daya daga cikin jami'o'i guda uku da Najeriya ta bude tsakanin 1961 zuwa 1962 sakamakon wani rahoto da wani kwamiti karkashin shugabancin Sir Eric Ashby ya gabatar wa gwamnati.

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin ne don yin nazari kan bukatun ilmin gaba da sakandire da na manyan makarantu a Najeriya cikin shekara 20 mai zuwa.

Haka zalika, da bukatar zafafa horas da kwararrun ma'aikata don sabuwar Najeriyar da ta samu 'yanci a burinta na samun bunkasar masana'antu cikin hanzari da habakar tattalin arziki.

A iya cewa Jami'ar Ibadan da Jami'ar Najeriya ta Nsukka ne kawai suka girmi Jami'ar Ahmadu Bello Zariya.

3. ABU na da sashe 99

Shafin the ABUSITE ya ruwaito cewa jami'ar a yanzu na da fadin hekta 7,000 da tsangayoyi guda 16 da cibiyar koyarwar gaba da digiri da sashe-sashe guda 99. Tana da cibiyoyin bincike guda biyar da cibiyoyin horar da kwararru guda shida da Sashen kula da Kwalejojin Aikin Gona da cibiyar koyon karatu daga nesa da makarantun firamare da sakandire da sauransu.

4. ABU ta bude ne da dalibai kasa da 450 Jami'ar Ahmadu Bello ta fara karatu ne da tsangaya hudu da sashe-sashe guda 15.

A cikin dalibai guda 426 da jami'ar ta bude da su, 147 ne kawai 'yan arewacin Najeriya.

Mulkin mallakar Birtaniya na sama da shekara 60, ilmi a arewacin Najeriya bai samu ci gaba sosai ba, idan an kwatanta da sauran sassan kudancin kasar guda biyu.

Dalibai kalilan ne daga arewa suka cancanci shiga jami'a, kuma 'yan arewa kalilan ne suka cancanci aikin koyarwa.

5. Dr. Ishaya Audu ne dan Najeriya shugaban ABU na farko Dr. Ishaya Shuaibu Audu, shi ne dan Najeriya na farko da ya shugabanci jami'ar Ahmadu Bello Zaria.

An haifi Ishaya Audu likitan yara kuma farfesa a Jami'ar Lagos, a Wusasa kusa da Zariya cikin 1928.

ABU a karkashin shugabancinsa ta bunkasa kuma ta samu ci gaba cikin sauri.

Ya fara shugabancin jami'ar ne daga 1966 zuwa 1975 bayan shugabanta na farko Farfesa Norman Alexander.

6. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato shi ne Uban ABU na farko Sir Ahmadu Bello (KBE), (GCON) Sardaunan Sakkwato shi ne Uban Jami'ar Ahmadu Bello Zariya na farko tun bayan kafa jami'ar a 1962 har zuwa 1966 shekarar da Allah ya yi masa rasuwa. Sauran Sarakunan da suka kasance ubannin ABU akwai:

Basarake Akenzua na II, Oba na Benin 1966–1972 Mai shari'ah Sir, Egbert Udo Udoma (KJW), Tsohon Alkalin alkalan Uganda kuma alkali a Kotun Kolin Najeriya 1972–1975 Cif Obafemi Awolowo, (CFR), Firimiyan Yammacin Najeriya 1975–1979 Lamido Aliyu Musdapha, (CFR), Lamidon Adamawa 1979–2010 Sa’ad Abubakar, (CFR), (mni), Sarkin Musulmi 2010–2015 Basarake Nnaemeka A. U. Achebe, (CFR), (mni), Obi na Onitsha 2015– Zuwa Yau

7. Jami'ar Ahmadu Bello Zariya ta yaye fitattun shugabanni maza da mata da manyan jami'an gwamnati ciki har da tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa 'Yar adua

Karin fitattun mutanen da jami'ar ABU ta yaye akwai:

1. Boss Gida Mustapha, sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya

2. Atiku Abubakar

3. Dr. Iyorchia Ayu shugaban jam'iyyar PDP mai ci

4. Danbaba Suntai

5. Marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albany Zaria

6. Alhaji Yayale Ahmed

7. Mai shari'ah Zainab Bulkachuwa tsohuwar shugabar kotun daukaka kara

8. Marigayi Mohammed Sanusi Barkindo tsohon babban sakataren OPEC

9. Afakriya Aduwa Gadzama tsohon babban daraktan DSS

10. Dr. Mahmud Tukur shugaban Jami'ar Bayero Kano na farko

11. Mallam Adamu Fika

12. Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli

13. Ghali Umar Na'abba

14. Mohammed Goni - gwamnan farar hula na farko a jihar Borno

15. Naja'atu Bala Mohammed mace ta farko da aka zaba shugabar kungiyar dalibai

16. Aisha Jummai Alhassan

17. Bunu Sheriff Musa

18. Farfesa Iya Abubakar

19. Zainab Shamsuna Ahmed

20. Adamu Adamu

8. Wasu fitattun mata da suka yi karatu a ABU kuma suka yi zarra

  • Farfesa Aisha Indo Mamman mace ta farko da ta zama likitar kimiyyar jini a arewacin Najeriya.
  • Farfesa Hajara Ibrahim mace ta farko da ta zama farfesa a fannin harhada magunguna a arewacin Najeriya.
  • Farfesa Ladi Adamu mace ta farko a arewacin Najeriya da ta zama farfesa a fannin yada labaran rediyo da talbijin.
  • Farfesa Gambo Laraba Abdullahi mace ta farko da zama shugabar jami'a a arewacin Najeriya.
  • Hajiya Hassu Iro Inko mace ta farko da aka yi imani ita ce ta fara kammala digiri daga jihar Katsina.

9. Alƙaryar shirya wasannin kwaikwayo

10. Mata masu binciken nukiliya na farko a Najeriya

Jami'an bincike a Cibiyar ba da horo da bincike kan makamashi ta Jami'ar Ahmadu Bello, an yi imani su ne mata na farko da suka fara samun lasisin wucin gadi don sarrafa nukiliya daga Hukumar kula da harkokin Nukiliya ta Najeriya.

A ranar 25 ga watan Yulin 2022 ne, Hukumar kula da makamashin Nukiliya ta Najeriya ta bai wa Engr Safiya Aliyu da Malama Nana Fatima Abdulmalik lasisin zama ma'aikatan binciken nukiliya.

Ba da lasisin gudanar da na'urar sarrafa makamashin nukiliya ya dace da dokar kiyaye hadurran nukiliya da sinadarin radiyeshin bisa ka'idojin bai wa kowanne jinsi damar a tafi da shi cikin harkokin sarrafa nukiliya a duniya.