Kocin Chelsea na harin Aubameyang

Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Chelsea Thomas Tuchel ya ce a kodayaushe yana son ci gaba da kyakkyawar alaka ta kut da kut da Pierre-Emerick Aubameyang bayan zaman da suka yi a Borussia Dortmund.
Rahotanni na nuna cewa Chelsea na matukar sha'awar sayen Aubameyang daga Barcelona kafin ranar rufe kasuwar 'yan wasa, 1 ga watan Satumba.
A watan Fabrairu ne Aubameyang ya koma Barca bayan ya saba wani mataki na ladabtarwa a Arsenal.
Kuma Tuchel ya ce har yanzu yana da alaka da dan wasan bayan zamansu a Jamus.
''Ban taba samun wata matsala ba da shi,'' in ji Tuchel, ranar Juma'a, kafin wasansu na gida da Tottenham ranar Lahadi (karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya).
Sai dai kociyan ya ki yarda ya yi magana kan yuwuwar sayen dan wasan a wannan bazara.
Amma kuma yana sha'awar yin magana a kan zaman da suka yi da shi a Dortmund, inda dan Gabon din ya yi shekara biyar kafin y koma Arsenal a 2018.
Arsenal ta sayi Aubameyang a kan Fam miliyan 56 a watan Janairu na 2018, amma kuma sabanin da aka samu a tsakaninsu saboda saba matakin da'a da aka dauka a kansa, abin ya kai ga tube shi a matsayin kyaftin din kungiyar, wanda a dalilin haka ya bar kungiyar a kyauta.
An ruwaito kociyan Arsenal Mikel Arteta na cewa yana fatan Aubameyang zai samu kyakkyawar tarba idan ya koma London, saboda ya cancanci hakan.
Kafin wasan Arsenal a gida da Leicester ranar Asabar, (karfe 3:00 na rana agogon Najeriya), Arteta ya ce, "Abin da aka yi an yi shi ne domin kare martabar kungiyar, da kuma dora ta a kan gwadaben da ya fi dacewa."
Ya kara da cewa "Auba dan wasa ne na daban. Ya yi mana kokari sosai. Ina fatan zai samu kyakkyawar tarba [idan ya kom] saboda ya cancanci hakan.''
Aubameyang, mai shekara 33, ya ci kwallo 11 a wasan La Liga 17 bayan da ya koma Barcelona a kakar da ta wuce.
Chelsea ta sayi manyan 'yan wasa da dama a bana, cikinsu har da dan wasan Ingila Raheem Sterling daga Manchester City
Da dan bayan Brighton Marc Cucurella da kuma na Napoli Kalidou Koulibaly dan Senegal.











