Ban yarda na dumama benci ba a Man City - Sterling

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sterlin dan Ingila asalin Jamaica ya ce an rage sa shi a wasa a City saboda wasu dalilai na daban
An wallafa

Dan wasan gaba na Chelsea Raheem Sterling ya ce bai yarda ya rika zaman dumama benci ba ne a tsohuwar kungiyarsa Manchester City shi ne ya sa ya ga ya kamata ya kara gaba, ya bara Zakarun na Premier.

Tun kakar 2018-19 Sterling mai shekara 27, ya kasance ba ya samun buga wasannin Premier sosai daga farko a Manchester Cityn, inda a kakar da ta gabata sau 23 kawai aka sa shi daga farko.

Bayan ya shafe shekara bakwai a City, Sterling ya ce yana son ya fuskanci sabon kalubale a don haka ya tafi Chelsea a cinikin da ya kaya Fam miliyan 50 a watan da ya gabata.

Dan wasan na Ingila asalin Jamaica ya ce shi tun yana dan shekara 17 ya kasance ana sa shi wasa akai-akai tun daga farko.

Saboda haka bai ga ta yadda za a ce bayan da ya zo kan ganiyarsa a wasan na tamola ba a ce zai koma yana dumama benci, ya ce wannan abu ne da ya ga ba za ta sabu ba.

Ya kara da cewa burinsa shi ne ya yi kokarin ganin an samu sauyi a hakan, amma abin bai yuwuwa, shi ke nan mai kasancewa ta kasance.

Ya ce a matsayinka na dan-Adam kana kokarin cimma buri ne, ''to ganin cewa lokacin wasana a City ya takaita saboda wasu dalilai na daban,

''Sai na ce ba zan ci gaba da zama in bata lokacina ba, na ce ina bukatar dorewa a yadda nake, don haka ina bukatar sabon kalubale,'' in ji shi.

Liverpool ta sayo shi ne daga cibiyar renon 'yan wasa ta QPR a 2010, kuma ya kasance daya daga cikin fitattun 'yan wasanta a kakar 2012-13, kafin City ta saye shi a 2015 a kan Fam miliyan 49.

Sterling ya dauki kofin Premier da City da kofin League (Carabao a yanzu) sau biyar da kuma na hukumar kwallon Ingila, FA daya, sai dai kofin Zakarun Turai ya gagare su.

 Tun bayan da ya fara taka wa Liverpool, wasan Premier yana shekara 17, ya yi wasa 469, ya kuma yi wa Ingila wasa 77 .

A yanzu kuma yana burin zama jigo a Chelsea fiye da yadda ya kasance a Manchester City.