'Yadda aka kashe ƙaramin yaron da ke hannuna a lokacin harin Kenya'

Asalin hoton, Jewel Kiriungi/BBC
- Marubuci, Jewel Kiriungi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi
- An wallafa
Shammi Allu, wace aka harba sau biyar a harin da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi suka kai a wata kasuwa ta Kenya shekaru 10 da suka gabata, wanda ya sa ta dogara kan sandunan guragu wajen tafiya, ta sha alawashi hawa duste mafi tsawo a duniya, Everest.
A wata tattaunawar da ta yi da BBC, Allu mai shekaru 61, ta bayyana kwarin guiwarta, inda ta ce, "Hawa dutsen Everest babban abu ne a wajena, yana da matuƙar muhimmanci a gare ni."
"Hawan Dusten Everest da nake so na yi, ina so na isar da sakon zaman lafiya, da nuna fata ta gari, da jajircewa da kuma yafiya ne."
A ranar 21 ga Satumban 2013 ne Allu ta tsira daga daya daga cikin mafiya munin hare-haren masu iƙirarin jihadi a tarihin Kenya.
Mayakan kungiyar al-Shabab da ke da alaƙa da al-Qaeda dauke da muggan makamai ne suka kai samame kan babban makeken kantin saye da sayarwa na Westgate da ke Nairobi, babban birnin kasar, inda suka mamaye shi na tsawon kwanaki hudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 67 tare da jikkata wasu sama da 200.
A lokacin harin, Allu tana aiki a matsayin mai gabatar da shirye-shirye a wani gidan rediyo a kasar, wanda ke gudanar da gasar cin abinci na yara yayin da tsakar rana suka ji karar harbe-harbe.
"Akwai wani karamin yaro a lokacin, wanda harbe-harben ya firgita sosai, ina ganin sa kawai sai na riƙe shi, na ce masa kar ya damu, ya zauna tare da ni, komai zai wuce." Allu ta ƙara da cewa kafin ka ce kwabo, kawai aka harbe yaron.
"Na sa hannuna a bayana, sai na ji alamun jiƙewa, ina dubawa kawai na lura cewa ni ma sun harbe ni a hannuna."
An harbe Allu a idon sawunta sau daya, a hannunta sau biyu kuma a bayanta sau biyu.
"Har yanzu ina tuno lokacin da abin ya faru, abu ne mai ban tsoro, ga warin jini ko ina." In ji ta.

Asalin hoton, Jewel Kiriungi/BBC
Mutane suna ta faɗawa kan junansu yayin da suke kokarin tserewa lokacin harin, bayan 'yan dakiku, wani bam ya tashi, kuma a nan ne inda aka harbe ta da ɗan yaron, a nan take yaron ya mutu a hannunta, in ji Allu.
Ta ƙara da cewa hakan na faruwa nan take ta ji zuciyarta ta karaya, sannan ta tsorata.
"Ina ganin haka, sai na mayar da hankalina kan bishiyoyin da ke bayan Westgate, na yi tunanin idan nayi hakan, zai iya jin samun ƙarfi har na sami taimako." in ji Allu.
Bayan kimanin sa'o'i hudu da rabi ne jami'an tsaro da kungiyar agaji ta Red Cross suka ceto ta, kafin daga bisani aka kai ta asibiti inda aka fara mata magani.
Lamarin ya taɓa huhun Allu kuma ta kwashe shekaru biyu tana tafiya da sanda, yayin da kuma akwai ɓurɓushin gurneti a cikin gadon bayanta.

Asalin hoton, Jewel Kiriungi/BBC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarar 2018, wani ɗan kasar Sin Xia Boyu ya ba ta ƙwarin gwiwa, wanda ya zama mutum na farko da aka yanke wa ƙafafu kuma ya yi nasarar hawa dutsen Everest da ke ƙasar Nepal.
"Kokarin saka takalmin sawu-ciki ne kalubale na farko da na fuskanta domin ƙafata ta ƙi shiga, amma yanzu ina da buri, wanda shi ne hawa dusten Everest," in ji ta.
"Da na fara gwada tafiya, na fara ne da nisan kilomita ɗaya, lokacin ga zafi kuma da ɗangeshi, amma yanzu, ina tsammanin zan iya yin tafiyar kusan kilomita 11."
Kafin harin, Allu ta kasance mai hawan dutse mafi tsayi a Kenya, wanda shi ne na biyu mafi tsawi a Afirka. Akan ɗauki kwanaki biyar zuwa bakwai kafin a kai ƙololuwar dutsen.
Allu na ganin cewa hawa dutsen Everest da ya shahara a duniya a matsayin wata dama ta jan hankalin jama'a kan mahimmancin muhalli.
Ta kara da cewa "Ina fatan zan iya yin magana game da kiyaye muhalli domin itatuwa ne suka ceci rayuwata a ranar."
Abubuwan da Allu ta fuskanta sun zo daidai da na Valentine Kadzo, wata wadda ita ma ta tsira daga harin.

Asalin hoton, Jewel Kiriungi/BBC
Valentine Kadzo, mahaifiyar yara huɗu na cikin aiki a wani shagon sayar da kayayyaki lokacin da aka fara harbe-harben.
Bayan ɗan lokaci kaɗan kawai ta ce sai ta ji an harbe ta yayin da take neman inda za ta ɓoye daga masu harbin.
"Ina jin an harbe ni, kawai sai na fara addu'a, ina roƙon Allah ya ceci rayuwata saboda ba na son na mutu."
Bayan kwana uku a asibiti aka sallami Kadzo, raunukan da ta samu ba su warke ba.
Harin ya kuma shafi iyalan waɗanda suka tsira. Mutane da yawa sun shiga cikin jimami da damuwa ganin halin da ƴan uwansu ke ciki da raunuka, wasu ma kamar ba za su rayu ba.
Ciki harda Iyalan Allu, mahaifinta da ƴar uwarta duk sun shiga cikin damuwa da jimami kasancewar su ne masu kula da ita bayan harin.
"Mahaifina ya kasance mutum mai matukar ƙwazo da karfi, manomi ne mai aiki da himma, amma lamarin ya jefa shi cikin damuwa da ƙunci, ƙodarsa ta fara gazawa, jininsa na yawan hawa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa."
Mutum biyu ne kawai aka yanke wa hukunci kan wannan ta’asa.
An yanke wa Mohammed Ahmed Abdi hukuncin zaman gidan yari na shekaru 33 da Hussein Hassan Mustafa daurin shekaru 18 bisa samun su da laifin taimaka wa kungiyar ƴan ta'addan.
A yayin shari’ar tasu, jihar ta ce ‘yan bindiga huɗu ne suka kai samamen, kuma an samu gawarwakinsu a cikin ɓaraguzan ginin kantin.
Don magance damuwar da ta shiga, Allu ta fara wani shiri mai suna "Trees for Peace."
Ta yi hadin gwiwa da kungiyoyi irin su Rotary Club a garinsu na Nanyuki don dasa bishiyoyi a fadin Kenya inda aka shuka sama da itatuwa 5,000 ya zuwa yanzu.












