Akwai rashin tabbas game da makomar Pochettino, Man U za ta cefanar da 'yan wasa da dama

Asalin hoton, Getty Images
Akwai rashin tabbass game da makomar kocin Chelsea Mauricio Pochettino bayan da kungiyar ta sha kaye a hannun Liverpool a wasan karshe na gasar cin kofin Carabao kuma ana ganin kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim ne zai maye gurbinsa . (Mail)
Manchester United za ta sayar da 'yan wasanta da dama a wannan bazara inda dan wasan gefe na kasar Brazil Antony, dan shekara 24 , na cikin wadanda za ta cefanar . (MEN)
Chelsea na son ta sayar da mai tsaron bayan kungiyar, Trevoh Chalobah, mai shekara 24 da dan wasan gaban Albania Armando Broja, yayin da akwai rashin tabbas game da makomar dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher, dan shekara 24, da dan wasan baya ta gefe hagu na Sfaniya Marc Cucurella, dan shekara 25, yayin da take shirin gudanar da sauye- sauye a wannan bazara. (Telegraph - subscription required)
Bayern Munich da Liverpool da Arsenal na rige -rigen siyan dan wasan tsakiya na Fulham da Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28 ,a wannan bazara. (Football Insider)
Dan wasan tsakiya na Manchester City Kevin de Bruyne ya fi son ya koma taka leda a MLS ta Amurka a maimakon Saudiyya. Dan wasan kasar Belgium zai cika shekara 33 a wannan bazara a lokacin da kwantaraginsa zai shiga shekara ta karshe . (Athletic - subscription required)
Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane, mai shekara 51, na sha’awar aiki a Italiya kuma ana ganin shahararren dan wasan Faransa zai koma Juventus. (La Gazzetta dello Sport in Italian)
Mai tsaron gidan Ingila Aaron Ramsdale, mai shekara 25, na son ya bar Arsenal a wannan bazara bayan da aka dauko mai tsaron ragar Sfaniya David Raya mai shekara 28 a matsayin wanda zai maye gurbinsa . (Football Insider)
Tottenham ce a gaba a zawarcin da ake yi wa dan wasan Hull City Jaden Philogene, dan shekara 22, duk da cewa Aston Villa za ta iya siyan dan wasan gefen Ingila a tawagar kwallon kafa ta masu shekara 21 (Teamtalk)
Watakila dan wasan Ingila Omari Forson,dan shekara 19, ya bar Manchester United a wannan bazara , saboda kwataragin dan wasan tsakiya a Old Trafford zai kare . (Athletic - subscription required)
Celtic na son ta dauko mai tsaron gidan Liverpool da Jamhuriyar Ireland Caoimhin Kelleher, dan shekara 25. (Football Insider)
Dan wasan tsakiya na Nice da Faransa Jean-Clair Todibo, mai shekara 24, na son ya koma Barcelona duk da cewa Manchester United na son ta dauko shi. (90min)











