Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal za ta bayar da ɗan wasa da kuɗi kan Bruno, Liverpool da Chelsea sun yi wa Oliseh rufdugu
Lazio na daga cikin kungiyoyin Italiya da ke zawarcin Mason Greenwood, Arsenal za ta iya yin tayin bayar da dan wasa da kudi kan Bruno Guimaraes sannan Liverpool ta shiga sahun masu neman Michael Olise.
Lazio ta fara tattaunawa da Manchester United don siyan tsohon dan wasan gaban Ingila Mason Greenwood, mai shekara 22, a kan kudi fam miliyan 30 (Mail)
Juventus da Napoli suma suna cikin masu fafutukar daukar dan wasan (Independent)
Arsenal na iya tayin ba da dan wasa da kudi don siyan dan wasan tsakiya na Newcastle dan kasar Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 26. (Football Transfers)
Liverpool na son doke Chelsea da Manchester United wajen siyan dan wasan Faransa Michael Olise, mai shekara 22, daga Crystal Palace. (Football Transfers)
Tottenham ta sha gaban Aston Villa a fafatukar sayen dan wasan tsakiyar Amurka Weston McKennie, mai shekara 25, daga Juventus. (Football Insider)
Dan wasan gaba na Athletic Bilbao dan kasar Sifaniya Nico Williams, mai shekara 21, ya ci gaba da dagewa kan aniyarsa ta zuwa Barcelona, duk da tattaunawa da Villa da Arsenal da Liverpool da kuma Newcastle United. (HITC)
AC Milan na sa ido kan Matty Cash na Villa amma yanzu abokan hamayyarsu Inter Milan suna tunanin daukar dan wasan bayan na Poland, mai shekara 26, a matsayin wanda zai maye gurbin Denzel Dumfries na Netherlands, mai shekara 28. (Sky Sport Italia)
Dan wasan tsakiya na Ingila Keira Walsh, mai shekara 27, na dab da komawa Arsenal daga zakarun Turai Barcelona. (90mint)
Chelsea na zawarcin dan wasan gaba na Atletico Madrid dan kasar Sifaniya Samu Omorodion da dan wasan Aston Villa dan kasar Colombia Jhon Duran, amma za su sayi daya daga cikin 'yan wasan masu shekaru 20 ne. (Fabrizio Romano)
Manchester United na kara matsa kaimi wajen neman karfafa ‘yan wasan kungiyar, inda dan wasan gaban Lille na Canada Jonathan David, mai shekara 24, ke kan gaba a jerin wadanda za su dauka. (inews)
Ba sabunta kwantiragin Bruno Fernandes bane babban abun da ya damu Manchester United a wannan bazara ba, duk da cewa ana alakanta dan wasan tsakiyar na Portugal, mai shekara 29, da Bayern Munich da Inter Milan. (Manchester Evening News)
Dan wasan tsakiya na Morocco, Sofyan Amrabat, mai shekara 27, ya shaida wa Fiorentina cewa ba ya son komawa kulob din bayan ya shafe kakar wasa ta bara a matsayin aro da Manchester United. (Athletic)
West Ham na da jan aiki a gabanta, don ci gaba da rike Mohammed Kudus a yayin da kulob din Al-Itihad na Saudiyya ke zawarcin dan wasan na Ghana mai shekara 23. (ESPN)
Leicester City da Fulham na zawarcin dan wasan Roma Edoardo Bove amma abokan hamayyarsu a Premier wato Everton da Bournemouth ma sun kara kaimi wajen neman dan wasan tsakiyar na Italiya mai shekara 22. (HITC)
Southampton ce kan gaba cikin wadanda suka fi damar dukar Flynn Downes a kan yarjejeniyar dindindin bayan da dan wasan tsakiyar na Ingila, mai shekara 25, ya tafi aro daga West Ham a bara. (GiveMeSport)