Chelsea na son Openda, Man United na tunanin ɗaukar Martinez

An wallafa

Chelsea tana sha'awar dan wasan gaban Belgium Lois Openda, Borussia Dortmund na son Pascal Gross na Brighton, Southampton na sha'awar sake siyan Danny Ings.

Chelsea na sha'awar daukar dan wasan gaban RB Leipzig dan kasar Belgium Lois Openda mai shekaru 24. (Teamtalk)

Borussia Dortmund na fatan daukar dan wasan tsakiyar Brighton dan kasar Jamus Pascal Gross, mai shekara 33, zuwa kasarsa ta haihuwa a wannan bazarar. (HITC)

Southampton ta yi tambaya game da sake siyan Danny Ings daga West Ham kuma a shirye take ta biya £6m ga tsohon dan wasan na Ingila mai shekara 31. (Mail)

Manchester United na shawara a kan ko za ta nemi golan Genoa dan kasar Spain Josep Martinez, duk da cewa Inter Milan ta riga ta amince da yarjejeniyar sirri da dan wasan mai shekaru 26. (Rudy Galetti)

Everton ta amince da daukar dan wasan tsakiyar Ingila Tim Iroegbunam, mai shekara 20, daga Aston Villa. (Football Insider)

Leicester City na dab da nada tsohon kocin Chelsea da Brighton Graham Potter a matsayin sabon kocinta. (Sun)

Ajax na son a rage mata farashin da Burnley ta yi wa dan wasan gaban Netherlands Wout Weghorst, mai shekara 31. (Telegraph)

West Ham na son dauko dan wasan Sunderland dan kasar Ingila Jack Clarke mai shekara 23 a wannan bazarar. (Football Insider)

Arsenal na ba da fifiko wajen karfafa 'yan wasan tsakiya bayan da ta rasa dan wasan gaban RB Leipzig na Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21. (Athletic}

Sheffield United ta fara tattaunawa da Nottingham Forest kan sayen dan wasan baya na Ingila Joe Worrall, mai shekara 27. (Teamtalk)

Birmingham City na sha'awar sayen golan Ingila Ryan Allsop mai shekaru 32 daga Hull City. (Birmingham Live)

Manchester United ta ci gaba da zawarcin dan wasan Bologna dan kasar Holland Joshua Zirkzee, mai shekara 23, amma babbar hukumar da ke da hannu a duk wata yarjejeniya tana dagula lamarin. (Sky Germany)

Arsenal ta yi tayin dan wasan Estonia Karl Hein, mai shekara 22, a matsayin sabon mai tsaron gida na uku. (Caught Offside)

Chelsea na shirin yin watsi da tayin Atletico Madrid na neman dan wasan tsakiyar Ingila Conor Gallagher mai shekaru 24. (Sun)

Gallagher ya shaida wa Chelsea cewa ba za a tilasta masa barin kulob din a bazara ba, yayin da Atletico, Tottenham da Aston Villa ke zawarcinsa. (HITC)