Maniyyata 737 sun tashi daga Najeriya ranar Litinin duk da yajin aiki

..

Asalin hoton, NAHCON

An wallafa

Duk da yajin aikin da kungiyoyin ƙwadago ke yi a Najeriya wanda kuma ya haddasa tsaiko a filayen jirgin saman ƙasar, maniyyata Hajjin bana daga ƙasar na ci gaba da tashi zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, National Hajj Commission of Nigeria (Nahcon) ta ce aƙalla maniyyata 737 ne suka tashi a yau Litinin daga jihohin Kwara da Sokoto.

Nahcon ta ce jirgin Air Peace ne ya fara tashi a yau daga birnin Ilorin na jihar Kwara da mutum 311 da misalin ƙarfe 9:52 na safe.

Sai kuma wani jirgin Flynas da ya sake tashi da mutum 426 daga jihar Sokoto.

Alƙaluman da hukumar ta wallafa sun nuna cewa zuwa yanzu jimillar maniyyata 38,249 aka kwashe zuwa Saudiyya don gudanar da babbar ibadar ta addinin Musulunci.

Da farko dai maniyyata a Najeriya sun ta nuna damuwa dangane da ci gaba da jigilarsu zuwa ƙasar mai tsarki domin sauke farali.

Kafin samun labarin tashin maniyyatan na ranar Litinin ɗin dai sai da BBC ta nemi jin ta bakin hukumar alhazan kan tabbatacin yajin aikin ba zai shafi jigilar ba.

Hukumar alhazan Najeriya ta amsa tambayar

...

Asalin hoton, Nahcon

Domin samun ƙarin haske kan halin da ake ciki da kuma amsar wannan tambayar, BBC ta tuntuɓi Fatima Sanda Usara, jami'ar hulɗa da jama'a ta hukumar alhazai ta ƙasa, inda ta ce hukumar ba ta tunanin yajin aikin zai shafi jigilar maniyyatan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Muna da fahimtar cewa wannan yajin aikin ba zai shafi yadda muke kwashe alhazai zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji ba saboda shi aikin hajji abu ne da yake da ƙayyadadden lokaci."

"A yau ɗin nan ma akwai jiragen da suka tashi daga Ilorin da kuma Jigawa." In ji Fatima.

Jami'ar hulɗar ta ƙara da cewa hukumar ta san da cewa "ana iya samun ɓata garin da za su iya haifar da cikas don kansu ba wai don hukumomin filayen jirgin sama sun yarda da hakan ba."

"Amma game da wannan yajin aiki, muna nan muna magana da ma'aikatan filayen jirgin sama kuma in sha Allahu ba za a samu wannan cikas ɗin ba." Ta ƙara haske.

Da BBC ta tambaye ta hanyar da hukumar alhazan za ta bi wajen kiyaye yajin aikin kar ya shafi yadda ake kwashe alhazai zuwa Sauddiyya ganin yadda jami'an ƙungiyoyin ƙwadago ke bin ofisoshi da filayen jiragen sama suna rufe su kamar yadda suka rufe filayen jiragen sama na Legas da na Abuja, Jami'ar hulɗa da jama'ar sai ta ce.

"Ɓangaren da ake ɗiban alhazai ba ɗaya ba ne da ɓangaren da ake kwashe sauran matafiya zuwa sauran ƙasashe, ɓangaren alhazai daban ne, aikin hajji ba ɗaya ba ne da sauran tafiye-tafiye, saboda haka muna da kyakkyawar fahimtar wannan yajin aikin ba zai shafi alhazanmu ba."

'Alaƙarmu na da kyau da ƴan ƙwadago'

Fatima ta ce hukumar Alhazai na da yarjejeniya da filayen jirgin sama inda ta ƙara da cewa suna kyautata zaton cewa ƙungiyar ƙwadago suna sane da cewa aikin hajjin ba ɗaya yake da sauran tafiye-tafiye ba.

"An san da cewa musulmai ba sa ɗaukar aikin hajji da wasu da kuma muhimmancinsa a wurinsu, su kansu ƴan ƙungiyar ƙwadagon suna da wannan masaniyar."

Ta kuma ce shuwagabannin hukumar na magana da ɓangarori daban-daban yadda ya kamata saboda haka ta ce suna tunani wannan yajin aikin ba zai shafi ko dakatar da jigilar alhazai ba.

"Ko da yaushe akwai manyan da za su tsaya su kula da wannan aikin."

"Yanzu dai muna da wannan tabbaci na cewa alhazanmu in sha Allahu za su tafi ba tare da samun wani cikas ba." In ji Fatima.

Daga ƙarshe Fatima Sanda ta kuma ce hukumar alhazai ba ta da wani fargabar cewa ma'aikatan filayen jirgin sama suma za su tsunduma cikin yajin aikin.