Rashford ba zai buga wa Man United wasa da Sheriff ba

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Manchester United, Marcus Rashford ba zai yi wa kungiyar wasan Europa League da za ta kara da Sheriff Tiraspol ranar Alhamis ba.
Mai shekara 24, wanda ake hasashen za a gayyace shi tawagar Ingila a lokacin da Gareth Southgate zai bayyana 'yan wasa ranar Alhamis, shi kuma zai yi jinya.
Kociyan United, Erik ten Hag bai fayyace ranar da Rashford zai dawo fagen fama ba.
Rashford wanda rabon da ya yi wa Ingila tamaula tun wasan karshe da Italia a Euro 2022, ya ji rauni a karawar da ya ci Arsenal kwallo biyu a gasar Premier.
Bai yi wa United wasan da Real Sociedad ta doke United 1-0 ba a Old Trafford a makon jiya a wasan farko a cikin rukuni a Europa League.
Kociyan United, ya ce ya zama wajibi su saka kwazo a wasa da Sheriff, wadda ta taba doke Real Madrid a Champions League.







