Magoya bayan Liverpool za su kai Uefa kotu

Asalin hoton, PA Media
Sama da magoya bayan Liverpool 1,700 ne ke shirin daukar matakin shari'a kan Uefa da cewar an kuntata musu a wasan karshe a Champions League.
Real Madrid ce ta lashe kofin Zakarun kuma na 14 jumulla, bayan da ta doke kungiyar Anfield a Faransa a kakar da ta wuce.
Hukumar kwallon kafar Turai na fuskantar matakan shari'a da magoya bayan Liverpool kan wasan da aka kara a birnin Paris.
Ba a fara wasan da wuri ba kamar yadda aka tsara har ta kai an yi lattin minti 35, inda Uefa ta ce ta ci karo da kalubalen matakan tsaro a ranar.
Wani kamfanin lauyoyi da ke Birmingham ya ce ya tattauna da mutane da yawa wadanda suka sha wahala a dalilin wasan har da jin ciwo da wasu suka ji.
Tuni sun yi shirin hadin gwiwa da wani babban kamfanin lauyoyi mai suna Pogust Goodhead don wakiltar mutum 1,450 da cewar Uefa ta yi sakaci.
Lauyoyin sun ce za su shigar da karar cewar Uefa ta karya dokar sayar da tikiti da kasa kula da lafiyar 'yan kallo da ta kai wasu suka jikkata a Paris.
Magoya bayan Liverpool da dama sun yi bayani kan yadda suka dade a kan layin shiga kallon wasan da 'yadda jami'an tsaro suka musguna musu har da bada barkonon tsohuwa.
A ranar wasu wadanda suka sayi tikiti ba su samu damar shiga kallon fafatawar ba, sakamakon turmutsisin mutane.

Asalin hoton, PA Media









