UEFA Super Cup: 'Yan wasan Real da za su kara da Frankfurt

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta fafata da Eintracht Frankfurt a Uefa Super Cup da za su kara ranar Laraba a Helsinki, Finland.
Ana buga wasan ne tsakanin wadda ta lashe Champions League da wadda ta dauki Europa Cup a kakar da ta wuce.
A bara ne Real Madrid ta lashe Champions League na 14 jumulla, bayan da ta ci Liverpool 1-0 a wasan karshe a Faransa.
Ita kuwa Frankfurt nasara ta yi a kan Rangers a bugun fenariti da ci 5-4, bayan da suka tashi 1-1 har da karin lokaci, inda kungiyar Bundesliga ta dauki Europa Cup na biyu a tarihi.
Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin za su fafata a tsakaninsu, tun bayan 1960 da Real Madrid ta doke Frankfurt da ci 7-3 a Hampden Park a Glasgow a gasar.
Alfredo Di Stefano ne ya ci wa Real kwallo uku, sannan Ferenc Puskas ya ci hudu, ita kuwa kungiyar Jamus ta ci ukun ta hannun Richard Kress da kuma Erwin Stein da ya ci biyu.
Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da za su buga wa Real karawar, wadda ke fatan lashe kofin farko a kakar bana.
'Yan wasan da za su buga wa Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Luis Lopez.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger, F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., Tchouameni, D. Ceballos, Camavinga.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.
Real Madrid me fatan daukar kofi shida a kakar nan ta lashe La Liga da Spanish Super Cup da kuma Champions League a kakar da ta wuce.
Batun da masu horarwa biyu suka fada

Asalin hoton, Getty Images
Carlo Ancelotti, kociyan Real Madrid: "A bara Eintracht ta yi wata bajinta ta ban mamaki, saboda ba sa cikin wadanda aka yi hasashen za ta dauki kofn. Sun buga kwallo mai kayatarwa sun doke Barcelona a Camp Nou a salon wasa mai zafi. Kungiya ce da za ta iya bayar da matsala, Barka muna da kwarewar da muke bukata, wasan zai kayatar.''
Oliver Glasner, mai horar da Frankfurt: "Mun kagu mu hadu da su. Bana ganin wasan cewar zan yi kan-kan-kan da Carlo Ancelotti, illa zan fuskanci Real, daya daga fitatciyar kungiya mai dunbin tarihi a fannin taka leda a duniya. Muna shiryawa kan yadda za mu samu damar lashe wasan.''
Jerin wadanda suka lashe Uefa Super Cup a tarihi
- FC Barcelona 5
- AC Milan 5
- Liverpool 4
- Real Madrid CF 4
- Atletico Madrid 3
- Ajax Amsterdam 3
- Chelsea 2
- Bayern Munich 2
- Valencia 2
- Juventus 2
- RSC Anderlecht 2
- Zenit St. Petersburg 1
- Sevilla 1
- Galatasaray 1
- SS Lazio 1
- Parma 1
- Manchester United 1
- KV Mechelen 1
- FC Porto 1
- Steaua Bucarest 1
- Aberdeen 1
- Aston Villa 1
- Nottingham Forest 1
- Dinamo Kiev 1









