Iran ta kai hari cikin Pakistan

..

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Iran ta bayyana cewa ta kai hare-hare kan sansanonin ƴan bindiga a yammacin ƙasar Pakistan.

Wannan ne karo na uku da ƙasar ke kai hari kan wata ƙasa a cikin mako ɗaya, inda a baya ta kai hari a Iraqi da Syria.

Kafar yaɗa labaru ta gwamnatin Iran ta ce hare-haren sun faɗa kan sansanoni biyu a Balochistan, waɗanda ake alaƙantawa da ƙungiyar ƴan bindiga ta Jaish al-Adl.

Jami'ai a Pakistan sun ce hare-haren sun kashe yara biyu tare da raunata mutum uku.

Pakistan ta ce hare-haren ta sama 'abu ne da ya saɓa wa doka' kuma ta yi gargaɗin cewa hakan zai iya janyo 'martani mai tsanani.'

Wannan lamari na zuwa ne a lokacin da zaman ɗarɗar a gabas ta tsakiya ke ƙaruwa, bayan da aka kwashe sama da kwana 100 Isra'ila na ruwan wuta kan Gaza bayan harin Hamas, da hare-haren da Amurka da Birtaniya suka kai a Yemen, inda mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran suka riƙa kai wa jiragen ruwa hari a tekun Maliya.

Harin da Iran ɗin ta kai a cikin Pakistan ya faɗa ne kan wani ƙauye da ke kan lardin Balochistan, wanda ke a kan iyaka ta ɓangaren iyakar ƙasar da ke kudu maso yammaci.

Iran ta ce ta kai harin ne kan mayaƙan ƙungiyar Jaisha al-Adl, ta ƴan ƙabilar Baloch mabiya Sunni, waɗanda suka riƙa kai hare-hare a kan dakarun Iran da na Pakistan.