Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Isra'ila ke shirin ƙaddamar da hari kan mafakar Falasɗinawa ta Rafah
Za a shiga wani yanayi na bala'i a birnin Rafah da ke Kudancin Gaza inda Isra'ila ta kaddamar da gagarumin hari a can, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargadi.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya umarci sojoji su shirya kwashe farar hula daga Rafah gabanin yakin da Isra'ila za ta fadada a kan Hamas.
Isra'ila ta ta kai hare-hare ta sama a birnin cikin daren 11 ga watan Fabarairu inda akalla mutum 67 suka mutu, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas. Isra'ila ta ce an yi lluguden wuta domin kai samamen da ya taimaka wajen sakin mutum biyu da aka yi garkuwa da su.
Isra'ila ta ce Rafah ne cibiya ta ƙarshe ga mayakan Hamas sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fiye da rabin al'ummar Gaza sun tsere kuma ita ce muhimmiyar matattara ta ayyukan jinƙai.
Yayin da kasashen duniya ke gargadi kan kai hari a Rafah, mun duba birnin da mutanen da ke samun mafaka a wajen da kuma tarihinsa.
A ina Rafah yake?
Rafah birni ne da ke kudancin Gaza. Yankin Rafah ya hada iyaka da Masar da Isra'ila - birnin a karan kansa yana kan iyakar Gaza da Masar.
An kiyasta yawan al'ummar wajen sun kai Falasɗinawa miliyan daya da rabi - ninki biyar fiye da soma hare-haren Isra'ila a zirin.
Yankin Rafah na da girman 60 sq km, girman garin Manhattan a New York.
Iyaka tilo da ta hada zirin Gaza da Masar na cikin Rafah kuma an shafe shekaru ana amfani da ita wajen shigar da agaji zuwa Gaza. Kafin yaƙin, ɗaruruwan manyan motoci sun yi amfani da wannan hanyar wajen shiga zirin Gaza a kullum.
A baya, akwai bututai da dama na safara a karkashin iyakar, da aka yi amfani da ita wajen zuwa ga wurin da Isra'ila da Masar suka rufe lamarin da ya taƙaita shigar da kaya zuwa Gaza. Wannan ya sa Rafah ta zama muhimmin waje ta fuskar kasuwanci da tattalin arziki.
Babu tabbaci kan yawan bututan da suka rage amma sojin Masar sun ce ya kawo karshen safarar kaya tare da lalata bututan a shekarun baya-bayan nan.
Tarihin Rafah
Rafah ɗaya ne cikin daɗaɗɗun biranen Gaza masu tarihi kuma ya kasance a ƙarƙashin mulkin Birtaniya daga 1917 zuwa 1948 lokacin da aka kafa ƙasar Isra'ila.
An samu ɓarkewar yaƙi da Larabawa sannan lokacin da aka kammala rikicin, Rafah tare da sauran zirin Gaza, sun faɗa ƙarƙashin ikon Masar.
A yaƙin 1967 - da aka fi sani da yaƙin kwana shida - Isra'ila ta mamaye birnin kamar yadda ta yi wa Gaza da yankin Sinai na Masar ƙawanya, sai Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da tuddan Golan da Gabashin Ƙudus.
Daga bisani a 1979, Masar da Isra'ila sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da a ƙarƙ ashinta aka mayar da Sinai zuwa Masar. An raba Rafah, wani ɓangare na Masar, ɗaya ɓangaren a Gaza da Isra'ila ta mamaye.
Kamar sauran yankunan Gaza, Rafah gida ne ga dubban Falasɗinawa yan gudun hijra da suka tsere ko aka tilastawa ficewa daga gidajensu lokacin yaƙin 1948 da kuma danginsu.
Yanayin birnin a yanzu
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da rabin al'ummar Gaza na cunkushe a Rafah inda Martin Griffiths, jami'in jin ƙai na MDD ya bayyana yanayin rayuwa a birnin a matsayin mummuna.
"Sun rasa abubuwan da suke buƙata na yau da kullum domin rayuwa, suna fama da yunwa, cututtuka da mutuwa," in ji shi.
Mutanen da aka ɗaiɗaita na rayuwa a kan titi da makarantu da tantuna. Bincike kan hotunan tauraron ɗan adam da BBC ta yi ya nuna ƙaruwar yawan tantuna a Rafah tun bayan da yaƙin ya ɓarke.
Mutane da yawa a nan kamar Abu Rushdi Abu Daqin, sun tserewa yaƙi a arewaci bayan da sojin Isra'ila suka faɗa musu su koma kudanci.
"Mun ga garari," in ji Abu Daqin da yake faɗa wa BBC. "Na bar birnin Gaza zuwa Hamad sanan na tafi Khan Younis, daga Khan Younis zuwa Rafah. Amma har zuwa yaushe?" ya tambaya, bayan da ya samu labarin barazanar Isra'ila na fara yaƙi ta ƙasa.
Mutane da dama da aka ɗaiɗaita a Rafah sun shaida wa BBC cewa sun fi son zama a yammacin birnin kusa da tekun meditereniyan, saboda tsoron fuskantar mamaya daga yankin gabashi, kusa da iyaka da Isra'ila.
Tsirarun asibitoci ne ke buɗe har da babban asibitin Rafah da asibitin ƙwararru na Kuwait da asibitin Abu Youssef Al-Najjar, dukkan su ba su da magunguna kuma suna fama da rashin wuta.
Firaiministan Isra'ila Netanyahu na gargaɗin soma yaƙi ta ƙasa a Rafah duk da allawadan da ƙasashen duniya suka yi, galibin mutane a Rafah na irin wannan tambayar da Abu Daqin ya yi: "Dukkan 'yan Gaza suna nan. Ina za mu iya zuwa?"
Isra'ila ta ce tana neman rage illatar da farar hula a hare-harenta da aka ƙaddamar a matsayin martani ga hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai inda aka kashe mutum 1,200, aka kuma yi garkuwa da kusan mutum 250.