Ban ce zan bar PSG a Janairu ba - Mbappe

An wallafa

Kylian Mbappe ya ce bai taba cewar zai bar Paris St Germain a watan Janairu, ba bayan rahotan da ke cewar dan wasan zai bar kungiyar a bana.

A cikin watan Mayu dan kwallon tawagar Faransa mai shekara 23 ya saka hannu kan yarjejeniya mai tsoka, domin ci gaba da taka leda a PSG.

Tun a baya can an yi ta alakanta Mbappe, wanda ya lashe kofin duniya da Fransa a Rasha a 2018 da cewar zai koma Real Madrid buga tamaula.

''Ina cikin farin ciki a PSG,'' kamar yadda Mbappe ya bayyana, bayan tashi wasan Paris St Germain da ta ci Marseille 1-0 ranar Lahadi a karawar mako na 11 a Ligue 1.

Shi ne ya bai wa Neymar kwallon da ya ci, kuma na 200 da dan wasan tawagar Brazil ya zura a raga a lik tun daga Santos da Barcelona da PSG.

''Ban taba cewar zan bar PSG a watan Janairu ba.''

Wani rahoto ya bayyana a lokacin da PSG za ta kara da Benfica a Champions League ranar Talata, inda aka ce Neymar baya jin dadin zama a PSG.

Rahoton ya kara da cewar kungiyar ta Faransa ta yi masa romon baka - zai bar PSG a watan Janairu, idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo.

Neymar ya ce ''Ban san dalilin wannan rahoton ba, wanda ya bayyana ranar da za mu buga Champions League.''

''Mutane za su dauka ina da hannu kan wannan lamarin, amma ba hannuna ko daya.''