Arsenal ta nace kan Gyokeres, Liverpool za ta ci riba da Klopp

Asalin hoton, Getty Images
Brentford na nazarin ɗauko ɗanwasan Norwich da Amurka mai shekara 24 Josh Sargent a yayin da ƙungiyar ke shirin rabuwa da ɗanwasan gabanta na Ingila Ivan Toney, mai shekara 27 wanda Chelsea da Arsenal ke hamayya. (Football.London)
Liverpool za ta fara tattaunawa da Andy Robertson kan sabunta kwantaraginsa duk da ba ta damu ba idan har ɗanwasan mai shekara 29 ya koma Bayern Munich da ake alaƙanta shi. (Football Insider)
Manchester City da Borussia Dortmund na sa ido kan matashin ɗanwasan gaba na AC Milan da Italiya Francesco Camarda. (Gazzetta dello Sport via Football Italia)
Chelsea na shirin biyan Brighton diyya kan Sam Jewell domin ɗauko ɗanwasan maimakon jira har zuwa bazara. (Sun)
Arsenal ta nace kan ɗanwasan gaba na Sporting Lisbon da Sweden mai shekara Viktor Gyokeres. (TodoFichajes - in Spanish)
Mahaifin Khvicha Kvaratskhelia ya ce yana so ya ci gaba da taka leda a Napoli duk da Real Madrid da Barcelona na farautarsa. (Radio Serie A via Mundo
Ɗanwasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot zai ƙarfafa sabunta kwangilarsa da Juventus maimakon raba gari da ƙungiyar a yayin da Tottenham ke farautarsa. (CaughtOffside)
Liverpool na fatan samun ribar fam miliyan 10 daga labarin rayuwar Jurgen Klopp da zai yi bankwana da Anfield a ƙarshen kaka. (Sun)
Arsenal na hamayya da Manchester United kan ɗanwasan baya na Girona da Spain Miguel Gutierrez. (Fichajes - in Spanish)











