Yaya aka yi ministocin Nijar suka fi Shugaban ƙasar kuɗi?

Asalin hoton, Presidence De La Republique Du Niger
Al'ummar Jamhuriyar Nijar na ci gaba da muhawara cikin mamaki game da irin tarin kadarorin da wasu ministocin ƙasar suka mallaka.
Rahoton kotu na shekara-shekara ya nuna cewa wasu ministoci a ƙasar sun mallaki dukiyar da ta kama daga mafi yawa saifa biliyan bakwai (N7bn) zuwa mafi ƙaranci saifa miliyan ɗari (N100m).
Kotun dai ta bayyana dukiyar da shugaban ƙasa da ministocin gwamnatinsa da 'yan majalisar dokoki da shugabanin hukumomi da sauransu suka ayyana cewa sun mallaka a shekara ta 2022.
'Yan Nijar da dama sun cika da mamaki ganin yadda wani ministan ƙasar, ba tare da wasu harkokin kasuwanci da suka bayyana a zahiri ba, ya mallaki irin wannan maƙudan kuɗi 'cikin ƙanƙanin lokaci'.
Mafi jan hankali a rahoton 2022 na dukiyar da jami'an gwamnati suka mallaka kamar yadda aka wallafa, shi ne yadda ministoci da dama suka fi Shugaba Mohammed Bazoum dukiya.
Rahoton ya ce dukiyar Shugaba Bazoum a shekara ta 2022 CFA 553,427,727 kwatankwacin naira miliyan 553 a kasuwar canji, inda ya samu ƙari a kan abin da ya mallaka bara waccan wato 2021, CFA 413,834,089 kimanin naira miliyan 413.
An sha zargin ministoci da manyan jami'an gwamnatin Nijar da cin hanci.
Shugaba Mohammed Bazoum da kansa ya ce manyan jami'ai kimanin 40 ne gwamnatinsa ta tuhuma tun bayan hawansa kan karagar mulki a 2021.
Haka zalika, kotu ta yanke wa wani tsohon ministan sadarwa, Zada Bawa hukuncin ɗauri a gidan yari, bayan ta same shi da laifin karkatar da kuɗaɗen kamfanin SOPAMIN.

Asalin hoton, Presidence De La Republique Du Niger
Kotun dai ita ce ke sa ido a kan kashe kuɗaɗen gwamnati a Jamhuriyar Nijar.
Doka ce ta tilasta wa duk wani jami’in gwamnati da muƙaminsa ya kai, ya bayyana dukiyar da yake da ita, kafin hawa kan wani muƙami.
Kuma dole jami'in ya riƙa sabunta bayanai duk shekara a kan dukiyar, matuƙar yana kan muƙamin, abin da ke bai wa al’umma damar sanin irin abubuwan da ke ƙaruwa a dukiyar jami'an gwamnati.
A cewar Micheal Zodi, shugaban wata ƙungiyar sa-ido a Nijar, siyasar ƙasar ce ta zama tamkar wani kasuwanci, inda ya yi zargin cewa ‘yan siyasar na azurta kansu da kuɗaɗen yi wa talakawa aiki.
Kiran a yi bincike - Masu gwagwarmaya
Micheal Zodi ya ce "Kwalliya ta biya kuɗin sabulu, daga cikin siyasa ne suka samu waɗannan kuɗaɗen tun da su ba ‘yan kasuwa ba ne. Kuma ba su gaji kuɗin daga ko'ina ba.
Tsirarun mutane ne masu kuɗi, amma talakawa suna fama da wahalhalu na rashin kuɗi da rashin abinci, in ji ɗan gwagwarmayar.
Ita ma ƙungiyar FSCN ta yi zargin cewa wasu jami'an gwamnati da karkatar da dukiyar ƙasa, abin da ya sanya su tara irin waɗannan maƙudan kuɗi.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Idi Abdu ya ce bai yi mamaki ba ganin yadda Nijar ke ci gaba da talaucewa.
Ya yi iƙirarin cewa "Da ka ga kasafin kuɗin nasu, ba za ka iya yin wata tambaya ba, sai ka ga cewa ai dole mu shiga halin talauci. Tun da kuɗin akwai inda suke tafiya, ɗan lokaci ƙanƙani kawai mutane sun azurta kansu".
Alhaji Idi Abdu ya ce ganinsa babu wani kasuwanci da jami'in gwamnatin Nijar ke yi da ya wuce siyasa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
'Yan Nijar da yawa ne ke nanata buƙatar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jamhuriyar Nijar (HALCIA) ta gaggauta shigin lamarin don yin bincike kan ‘yan siyasa da jami'an gwamnatin ƙasar.
Sai dai wani jigo a ƙungiyar matasan jam’iyyar PNDS Tarayya ya ce zarge-zargen da wasu ke yi cewa ta hanyar karkatar da dukiyar ƙasa da cin hanci da rashawa jami'an gwamnatin suka tara irin waɗannan kuɗaɗe rashin adalci ne.
A cewarsa ba gaskiya ba ne a ce jami'i ko ministan gwamnati da ya mallaki dukiya, ta haramtacciyar hanya kawai ya same ta.
Sahanin Muhammadu ya ce son rai ne kawai wasu ke faɗa game da ministocin jam'iyyar mai mulki. A cewarsa: "Wasu kawai na son ɓata wa wani ko wasu suna ne".
Sahanin Muhammadu ya ce ba zai iya cewa babu cin hanci a tsakanin jami'an gwamnatin ƙasar ba, don kuwa matsala ce da ake fama da ita ko'ina a duniya.
"Shugaban ƙasa tun lokacin da ya kama mulki, kokawa yake wajen yaƙar irin wannan matsala", in ji shi.
Rahoton na kotun kula da kashe kudaden gwamnatin dai ya bayyana cewa akwai wasu jami’an gwamnati da ke kan mulki waɗanda ba su yarda sun bayyana kadarorinsu ba.











