An dora karan tsana a kan Messi a PSG

Asalin hoton, Getty Images
An dauki karan tsana an dora a kan Lionel Messi daga magoya bayan Paris St Germain tun bayan da aka fitar da Paris St Germain daga Champions League a bana.
Haka kuma damar daukar Ligue 1 da PSG ke fata na kara dusashewa, bayan da ranar Lahadi Lyon ta doke ta 1-0 a gida.
Kyaftin din Argentina bai taka rawar gani ba a wasan, karo na biyu a jere da aka doke PSG a gida, kuma Messi bai ci kwallo ba.
PSG na fatan daukar Ligue 1 na 11 kuma na tara a kaka 12 tun bayan da attajirai daga Qatar da suka mallaki kungiyar.
Yanzu an rage tazarar maki tsakaninta da mai biye da ita Lens da Marseille zuwa shida, kuma saura wasa tara a karkare kakar nan.
Wannan ce kaka mafi muni da PSG ke fuskanta tun bayan 2001, kuma wasan gaba da kungiuar za ta yi shine a gidan Nice, wadda ba a doke ta ba tun shiga watan Janairun 2023.
Kenan kofin Ligue 1 kadai PSG ke fatan dauka a kakar nan, bayan da aka yi waje da ita a Champions League da French Cup.
Bayern Munich ce ta cire PSG daga gasar zakarun Turai ta bana, bayan nasara gida da waje, kofin da kungiyar Faransa ke fatan dauka a karon farko.
''Duk kakar da aka fitar da PSG daga Champions League sai su koma daukar sauran wasanni da rashin mahimmaci.'' in ji Vincent Duluc kamar yadda aka wallafa a L'Equipe.
Wasu na ganin cewar yi wa Messi ihu da kuwa a lokacin da Messi ya taba kwallo bai kamata, wanda ya ja ragamar Argentina ta lashe Kofin duniya a Qatar a 2022.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu magoya bayan kan dora alhakin rashin kokarin kungiyar a kan kyaftin din Argentina, bayan da ake ganin har yanzu ba a kammala gina PSG kamar yadda ya kamata ba.
L'Equipe ta ce ihun da ake yi wa Messi ya shafi yawo da yake yawan yi shi kadai a fili, maimakon yake guje-guje da sa kwazon karbar kwallo daga abokan karawa.
To sai dai ba a wannan kakar Messi ya fara yawace-yawace a cikin fili ba - wani bincike da aka gudanar a gasar kofin duniya a Qatar Messi ya yi tafiyar kilometre 14 kawai yana tafiya a cikin fila a wasa uku a cikin rukuni.
Sai dai wasu sun manta cewar ba tafiyar da Messi ke yi a cikin fili ne matsalar ba, illa shekaru sun ja, wanda a cikin watan Yuni zai cika shekara 36 a karshen yarjejeniyarsa da PSG, bayan kaka biyu.
Yanzu zabi na PSG ko za ta tsawaita zaman Messi, wanda shekaru suka ja da ci gaba da biyansa $43.6m a duk shekara a lokacin da Uefa ta saka mata ido kan kashe kudin kungiya daidai da abinda ta samu.
Watakila hankalin Messi ya koma kan wata kungiyar a kaka mai zuwa - wasu rahotanni na cewar Barcelona ta tuntubi PSG kan sake daukar kyaftin din Argentina.










