Ƙungiyoyin Saudiyya na farautar De Bruyne, Chelsea na son golan Arsenal

An wallafa

Manchester City na fuskantar barazana daga ƙungyoyin Saudiyya da ke farautar ɗanwasanta na tsakiya mai shekara 32 na Belgium Kevin de Bruyne. (Mail)

Darajar ɗanwasan za ta iya zarta fam miliyan 100 kafin City ta yi tunanin sayar da De Bruyne. (Talksport)

Chelsea a shirye take ta sayar da golan Spain Robert Sanchez, mai shekara 26, a wannan bazara akwai kuma yiyuwar ta ɗauko golan Ingila Aaron Ramsdale, mai shekara 25, a madadinsa. (HITC)

Chelsea na farautar ɗanwasan baya na Faransa Jules Kounde, mai shekara 25, yayin da ƙungiyar ke tunanin tayin ɗanwasan na Barcelona. (Fichajes - in Spanish)

Arsenal na son ɗanwasan gaba na Juventus Kenan Yildiz, mai shekara 18, amma kuma ɗanwasan na Turkiyya, na cikin lissafin Liverpool da Borussia Dortmund. (Calciomercato - in Italian)

Everton na farautar ɗanwasan baya na Sunderland Ingila Dan Ballard, mai shekara 23, idan har Jarrod Branthwaite, mai shekara 21, ya bar Goodison Park a bazara. (Football Transfers)

Manchester United na nazarin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Real Betis Guido Rodriguez, mai shekara 29 yayin da ɗanwasan na Argentina kwangilarsa ke dab da kawo wa ƙarshe. (Fichajes - in Spanish)

Ƙungiyoyin Saudiyya Al-Ittihad da Al-Nassr na ribibin ɗanwasan baya na Manchester United da Faransa mai shekara 30 Raphael Varane. (90 min)

Manchester United na sa ido kan ɗanwasan baya na Juventus Gleison Bremer, mai shekara 26, domin maye gurbin Varane kuma za ta iya biyan tsakanin yuro miliyan 60 zuwa 70 kan ɗanwasan na Brazil. (Tuttosport - in Italian)

West Ham na shirin ware maƙudan kuɗi domin karɓo ɗanwasan gaba na Bournemouth mai shekara 26 Dominic Solanke. (Football Insider)

Manchester City na nazari kan ɗanwasan tsakiya na West Ham mai shekara 26 Lucas Paqueta idan har ɗanwasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva, mai shekara 29 ya bar ƙungiyar. (Telegraph - subscription required)

Matashin ɗanwasan Ingila Adam Berry, mai shekara 18 na shirin ƙulla yarjejeniya da Nottingham Forest bayan barin Manchester United. (Sky Sports)

Manchester United da Arsenal da Tottenham na ribibin ɗanwasan tsakiya na Fenerbahce mai shekara 24 Sebastian Szymanski. (Teamtalk)

West Ham da Crystal Palace na cikin ƙungiyoyin Ingila da ke son ɗanwasan tsakiya na ƙasar Olly Box, mai shekara 18, wanda ke taka rawar gani a Dartford. (HITC)

Makomar Matthijs de Ligt a Bayern Munich ta dogara ne da yanke shawarar wanda zai gaji Thomas Tuchel a matsayin koci yayin da ƙungiyoyin Ingila da dama ke son ɗauko ɗanwasan na baya na Netherlands. (Fabrizio Romano)