Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea za ta yi nazari kan makomar Pochettino, Flick zai koma Bayern Munich
Chelsea za ta yi nazarin karshen kakar wasa ta bana bayan wasan karshe na gasar Premier da za ta yi da Bournemouth, inda za ta yanke shawara kan makomar kocinta Mauricio Pochettino. (Telegraph)
Arsenal na zawarcin tsohon mai tsaron ragar kungiyar da Poland Wojciech Szczesny, mai shekara 34, da golan Brighton Jason Steele dan Birtaniya da kuma na Ajax Diant Ramaj dan kasar Jamus yayin da su ke neman wanda zai maye gurbin Aaron Ramsdale, mai shekara 25 wanda zai bar Gunners. (Standard)
Har illa yau Arsenal na kuma duba yiwuwar daukar golan Everton da Ingila Jordan Pickford, mai shekara 30 a wannan bazara. (Teamtalk)
Gunners na kuma neman dan wasan baya da tsakiya da kuma mai kai hari a kokarin da suke yi domin fadada 'yan wasan kungiyar karkashin jagorancin Mikel Arteta. (Standard)
Graham Potter ya ki amincewa da damar da aka bashi na zama kociyan Ajax, bayan da ya kasance wanda ke kan gaba a matsayin jagoran kungiyar ta Netherlands . (Athletic - subscription required)
Yar wasa mai kai hari ta Manchester United Nikita Parris ita ma ta yi watsi da tayin da aka yi mata na komawa North Carolina Courage da ke Amurka a watan Afrilun da ya gabata yayin da 'yar wasan Ingila mai shekara 30 ke son ta fafata a wasan karshe na gasar mata ta FA da Tottenham. (Athletic - subscription required)
Bayern Munich na tattaunawa kan nada tsohon kocin Jamus Hansi Flick a matsayin sabon kocinta , yayin da tsohon kocin nata mai shekara 59 a shirye yake ya koma kan tsohon mukaminsa domin maye gurbin Thomas Tuchel. (Sky Sports Germany)
Dan wasan bayan Manchester City da Brazil Yan Couto, mai shekara 21 wanda aka bada shi aro gat Girona, na jan hankalin Bayern Leverkusen da Juventus da kuma wasu kungiyoyi Premier a kasuwar bazara. (Talksport)
Eintracht Frankfurt na son kudi yuro miliyan 50 zuwa 60 ga dan wasan baya na Ecuador Willian Pacho mai shekara 22 wanda aka danganta shi da Liverpool. (Sky Sports Germany)
Mutumin da ya mallaki Everton Farhad Moshiri zai yanke shawara a karshen mako game da tattaunawar da suke yi da kamfanin 777 Partners wanda suke son su sayi kungiyar bayan tattaunawar da suka yi game da wani rikici da ya kuno kai a baya baya nan. (Football Insider)
A wani labarin kuma kamfanin wasani na Amurka MSP Sports Capital,wanda ya nuna alamun yana son ya sayi Tottenham a bara an ce yana zaman jiran ya ga yadda za ta kaya idan tattaunawar da ake yi da kamfanin 777 kanToffees ta ruguje. (Football London)
Newcastle United ta tattauna da Dougie Freedman na Crystal Palace da Johannes Spors, wanda shi ne darekan wasanni na kamfanin 777 a kan mukamannsu na darektan wasani (Sky Sports)
Manchester City ta amince ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sayan dan wasan tsakiya na Amurka Cavan Sullivan, dan shekara 14 wanda ke taka leda a kungiyar Philadelphia Union na Major League Soccer a Amurka, idan ya kai shekara 18 . (ESPN)