Ƙoƙarin da Chelsea ke yi kwana biyu ya nuna irin abin da muka tsara tun farko - Todd Boehly

An wallafa

Mai ƙungiyar Chelsea Todd Boehly ya ce ƙoƙarin da kulob ɗin ke yi hujja ce cewa kwalliya "za ta biya kuɗin sabulu" a ƙarƙashin mai horarwa Mauricio Pochettino.

Chelsea ba ta yi rashin nasara ba cikin wasa uku da ta buga a jere, inda ta doke West Ham da Tottenham, bayan ta yi canjaras da Aston Villa.

Sakamakon sun taimaka wa ƙungiyar haurawa zuwa mataki na bakwai a Premier League, wanda zai iya ba ta nasarar zuwa gasar zakarun Turai, yayin da kuma tazarar maki biyu ce kacal tsakaninsu da Newcastle da take mataki na shida.

AN zargi Boehly da mayar da kulob ɗin wani abin "yi wa dariya" a watan Maris, amma Ba'amurken ya ce tsare-tsarensu sun fara kaiwa ga gaci.

Da yake magana a taron Sportico a Los Angeles ranar Laraba, Boehly ya ce: "Mun ga wasa biyu da rabi da suka wuce...a zagaye na biyu a Aston Villa, da Tottenham, da kuma West Ham inda muka buga wasa mai ƙayatarwa.

"Abin ya yi kyau, irin abin da muka tsara kenan, yadda muka dinga fara wasa daga baya, muka gina harin kuma muka matso gaba, cikin tsari sosai da kuma yawan shot ɗin da muka yi.

"A waɗannan wasannin, za ku gane irin abin da muka tsara da zai faru nan gaba."

Chelsea za ta buga wasanta na gaba da Nottingham Forest ranar Asabar, kafin ta ziyarci Brighton ranar 15 ga watan Mayu sannan kuma ta karɓi baƙuncin Bournemouth a wasan ƙarshe ranar 19 ga watan.

Chelsea's next game is at Nottingham Forest on Saturday,