Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Watakila Palmer ba zai buga wasan Arsenal ba
Watakila Chelsea za ta je gidan Arsenal buga Premier League a kwantan wasa ba tare da Cole Palmer ba.
Palmer tsohon dan wasan Manchester City, ya ci kwallo 20 irin yawan na Erling Haaland a da ya zura a raga a kakar nan.
Kociyan Chelsea, Mauricio Pochettino ya ce matashin mai shekara 21 bai warke ba daga rashin lafiya da ya kamu.
Arsenal ce ta daya a kan teburin Premier League, bayan da ta doke Wolverhampton 2-0 ranar Asabar a Molineux.
Chelsea tana ta tara a kan teburi da tazarar maki uku tsakaninta da gurbi na bakwai - kuma idan Palmer ba zai buga wasan ba, hakan zai amfani Arsenal.
Sai dai wasan zai karawa Gunners karfin gwiwa idan ta yi nasara a kan Chelsea, bayan da ta yi kaka 20 rabon ta da Premier League.
An yi waje da Arsenal daga Champions League na kakar nan, bayan da Bayern Munich ta fitar da ita, kenan Premier League kadai take fatan dauka a bana.
Ita kuwa Chelsea an fitar da ita daga dukkan kofuna, illa dai za ta yi kokarin samun gurbin shiga gasar zakarun Turai a badi.
Ranar Asabar, Manchester City ta yi waje da Chelsea a FA Cup a daf da karshe, tuni Liverpool ta doke ta a wasan karshe a Carabao Cup.
Wannan shi ne wasa na hudu a kwana 10 da Arsenal za ta yi wasa, amma Mikel Arteta ya ce a shirye suke da fuskantar kowanne kalubale.