An kawo karshen Man City bayan wasa 32 a jere ba a doke ta ba a lik

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Bournemouth a wasan mako na 10 a Premier League da suka fafata ranar Asabar a Vitality.
Minti tara da fara tamaula Semenyo ya fara ci wa Bournemouth ƙwallo, kuma haka suka je hutu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, Bournemouth ta kara na biyu ta hannun Evanilson daga baya City ta zare ɗaya ta hannun Gvardiol, saura minti takwas a tashi wasan.
Kenan Josko Gvardiol ya ci ƙwallo na shida a wasan waje daga bakwai a Premier League.
Da wannan sakamakon Bournemouth ta kawo karshen Man City a wasa 32 a jere a lik ba tare da rashin nasara ba a babbar gasar tamaula ta Ingila.
City mai rike da Premier League ta ci karawa 26 daga ciki da canjaras shida, wadda rabon da ta yi rashin nasara a lik tun 1-0 a hannun Aston Villa ranar 6 ga watan Disamba.
Wannan shi ne karon farko da City ta buga karawa a waje ranar Asabar da karfe huɗu agogon Najeriya, tun bayan rashin nasara a Wolves a Satumbar 2023.
Erling Haaland wanda bai zura ƙwallo ba a ranar ta Asabar ya ci 74 a wasa 75 a Premier League, tun bayan da ya koma Etihad.
Saura ƙwallo ɗaya ya yi kan-kan-kan da Alan Shearer mai 75 a karawa 93 a matakin wanda ya ci da yawa a ƙarancin wasanni.











