Man United ta biya £14.5m ga Ten Hag da wa su jami'ai

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta biya £14.5m ga Erik ten Hag da daraktan wasanni Dan Ashworth da wasu tsoffin jami'anta.

United mai Premier League 20 jimilla tana fuskantar kalubale, wadda take ta 15 a teburin kakar nan, bayan da Tottenham ta doke ta 1-0 ranar Lahadi.

Sabon koci, Ruben Amorim ya kasa kamo bakin zare tun bayan da ya maye gurbin Ten Hag, wanda aka kora cikin Oktoba, bayan kwana 116 a kan aikin.

Tun kafin nan ƙungiyar Old Trafford ta tsawaita yarjejeniyar Ten Hag, domin ya ci gaba da jan ragama zuwa karshen kakar 2026 daga baya ta kore shi.

Hakan ya sa United ta hakura da Ashworth, daraktan wasanni wanda ya koma Old Trafford daga Newcastle United ranar 1 ga watan Yuli.

United ta sanar da biyan kuɗin ne a rahoton zangon karshen watan Disamba, inda ta biya Ten Hag £10.4m, saboda yarjejeniyarsa ba ta kare ba a ƙungiyar.

United na shirin kara rage ma'aikata duk da 250 da ta sallama a baya, domin samun karin kuɗin da za take gudanar da babbar ƙungiya.

Duk da United ta kara kuɗin farashin tikiti ta sanar da hasarar £27.7m a zangon karshe a watan Disambar.