Liverpool ta shirya karawar hamayya da Everton - Slot

Arne Slot

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arne Slot ya ce Liverpool a shirye take ta fuskanci Everton a ƙwantan wasan Premier League ranar Laraba a Goodison Park.

Wannan shi ne karo na 122 da za su kece raini a tsakaninsu a wasan na hamayya a Goodison Park da ake kira Mersyside Derby.

Slot ya kara da cewar a shirye suke su lashe fafatawar su koma kan ganiya, tun bayan fitar da su da Plymouth Argyle ta yi daga FA Cup na bana.

Tun farko an tsara buga wasan ranar 7 ga watan Disambar 2024, amma sai aka soke karawar, sakamakon gagarumar guguwa da mamakon zubar ruwan sama.

Everton za ta yi ban kwana da filin wasanninta na Goodison Park a karshen kakar nan, wanda ta fara tamaula a ciki tun 1892, za ta koma Bramley-Moore Dock.

Liverpool ce ta ɗaya a kan teburin Premier League da maki 56 da tazarar maki shida tsakani da Arsenal ta biyu, ita kuwa Everton mai maki 26 tana ta 16 teburin.

Wasan da suka kara a bara a tsakaninsu a Premier League:

Premier League ranar Laraba 24 ga watan Afirilun 2024

  • Everton 2 - 0 Liverpool

Premier League ranar Asabar 21 ga watan Oktoban 2023

  • Liverpool 2 - 0 Everton

A bara ne aka doke Liverpool 2-0 a Goodison Park a wasan karshe da Jurgen Klopp ya ziyarci Everton karkashin Sean Dyche.

Wanna karon Liverpool za ta je Everton tare da Slot, wanda ya maye gurbin Klopp kan fara kakar nan, shi kuwa David Moyes ya karɓi aiki daga Dyche.

Everton ta doke Brighton 1-0 da caskara Leicester City 4-0 a wasa biyu baya da ta kara a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Haka kum ƙungiyar Goodison Park ta yi wasa tara ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba, wadda take da wannan ƙwazon ita ce Liverpool da Nottingham Fores masu 10 kowacce.

Mai tsare baya, Joe Gomez ba zai buga wa Liverpool fafatawar ba, kuma da kyar ne idan Trent Alexander-Arnold zai yi wasan na hamayya in ji Slot.

Alexander-Arnold bai buga wa Liverpool wasa biyu baya ba, sakamakon jinya, shi kuwa Gomez ya ji rauni ranar Asabar a wasan da Plymouth ta fitar da Liverpool daga FA Cup.