Barcelona za ta buga wasa shida cikin watan Maris

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona za ta buga wasa shida a cikin watan Maris da ya haɗa da huɗu a La Liga da kuma biyu a Champions League.
Cikin wasannin babbar gasar tamaula ta Sifaniya za ta fara karawa ranar Lahadi da karɓar bakuncin Real Sociedad.
Daga nan Osasuna ta je gidan Barcelona ranar 8 ga watan Maris, sai kuma ta je Atletico Madrid mako ɗaya tsakani a La Liga.
Wasan karshe da Barcelona za ta buga a cikin watan Maris a La Liga, shi ne karɓar bakuncin Girona ranar 30 ga watan.
Sauran wasa biyu da za ta yi shi ne a Champions League, wanda za ta je Benficaa zagayen ƴan 16 wasan farko ranar Laraba 5 ga watan Maris.
Benfica za ta je wasa na biyu gidan Barcelona a gasar ta zakarun Turai wasa na biyu zagayen ƴan 16 ranar Talata 11 ga watan Maris.
Barcelona tana jan ragamar teburin La Liga da maki 54, iri ɗaya da na Real Madrid ta biyu da kuma Atletico Madrid mai maki 53 a mataki na uku.
Barcelona, wadda ta lashe Spanish Super Cup a bana, ta kai zagayen daf da karshe a Copa del Rey.
Ta kuma tashi 4-4 a wasan farko da Atletico Madrid ranar 25 ga watan Fabrairu, tana fatan kai wa zagayen gaba da zarar ta yi nasara a gidan Atletico ranar 2 ga watan Afirilu.
Wasannin da Barcelona za ta yi cikin watan Maris:
Spanish La Liga Ranar Lahadi 2 ga watan Maris
- Barcelona da Sociedad
Champions League Ranar Laraba 5 ga watan Maris
- Benfica da Barcelona
Spanish La Liga Ranar Asabar 8 ga watan Maris
- Barcelona da Osasuna
Champions League Ranar Talata 11 ga watan Maris
- Barcelona da Benfica
Spanish La Liga Ranar Lahadi 16 ga watan Maris
- Atl Madrid da Barcelona
Spanish La Liga Ranar Lahadi 30 ga watan Maris
- Barcelona da Girona











