Za mu lashe Premier da Champions Lig a bana - Saka

Asalin hoton, Getty Images
Bukayo Saka ya ce shi da abokan kwallonsa na Arsenal ba sa fargabar suce suna son lashe Premier da Champions Lig a bana.
Gunners ce ta riƙa zuwa ta biyu a Premier a shekaru biyun da Manchester City ta ce a baya, yanzu kuma tana ta uku a kan teburi - da maki shida tsakninta da ta ɗaya.
Sun koma Champions Lig a bara bayan shekaru shida da suka kwashe ba su halarci gasar ba, inda suka ƙare a wasan kusa da daf da na ƙarshe.
Yanzu shekara huɗu kenan rabon Arsenal da ta ci wani babban kofi, amma Saka ya ce yana fatan taimakawa Arsenal ta ga ta ci kofi a bana.
"Ba ma shakka. Kaka biyu da suka gabata mun ƙare gasar a matsayi na biyu mun yi kusa da ci," ya shaida wa BBC a wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi.
"Yanzu kuma mun sake dawowa Champions Lig - muna da wata wayewa a gasar yanzu, dan haka yanzu muna da kwarin giwar gwabzawa domin cin kowanne kofi.
"Yanzu muna son ɗaukar mataki na gaba mu gwada cin waki abu."
Bukayo Saka says he and his Arsenal team-mates are "not scared" of saying they want to win the Premier League or Champions League this season.
Saka na cikin tawagar Arsenal da ta lashe FA a 2020 sai dai kuma ya gaza cin Euro 2024 - sannan suka zo matsayi na biyu a Premier har sau biyu.
"In zan faɗi gaskiya abun tashin hankali ne," in ji shi.
"Abu ne da yake buƙatar ƙarin mayar da hankali. Ina ganin akwai buƙatar mu ɗaga wani abu a bana, tabbas".











