Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hamas ta bayyana sunayen sojoji mata huɗu da za ta saki ranar Asabar
Hamas ta bayyana sunayen mutane huɗu da take garkuwa da su waɗanda za ta sako ranar Asabar ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Mutanen huɗu waɗanda sojoji ne su ne Karina Ariev, Daniella Gilboa, Naama Levy da kuma Liri Albag.
Za a sako su ne domin yin musaya da Falasɗinawa 180 waɗanda ke tsare a hannun Isra'ila.
Wannan ne karo na biyu da za a yi musayar waɗanda Hamas ke garkuwa da su da Falasɗinawan da Isra'ila ke tsare da su a ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimmawa a ranar Lahadin da ta gabata.
An yi musayar mutum uku da ake garkuwa da su da Falasɗinawa 90 waɗanda ke tsare a Isra'ila a karo na farko jim kaɗan bayan fara aikin yarjejeniyar.
Yarjejeniyar ce ta dakatar da yaƙin da ake gwabzawa a Gaza, wanda ya samo asali a lokacin da Hamas ta kai hari kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Kimanin mutum 1,200 ne aka kashe a lokacin harin sannan kuma Hamas ta kwashe mutum 251 zuwa cikin Gaza, inda ta yi garkuwa da su.
Ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin Hamas a Gaza ta bayyana cewa an kashe sama da mutum 47,200 tun bayan fara yaƙin, waɗanda mafi yawancsu fararen hula ne.
Haka nan kuma ana sa ran Hamas za ta bayar da bayani kan mutum 26 da take garkuwa da su, wadanda ake sa ran sakin su a cikin makonni biyar masu zuwa.
Waɗanda suka haɗa da iyalin Bibas – iyaye biyu da yara biyu, inda ɗaya daga cikin yaran mai suna Kfir ke da wata 10 a duniya lokacin da aka yi garkuwa da shi, kuma shi ne mafi yarunta a cikin duk waɗanda Hamas ta ɗauke.
Babu ƙarin haske kan ko bayanan za su ƙunshi sunaye ko kuma kawai adadin mutanen da ake garkuwa da su da ke raye ko waɗanda suka mutu ne.
Falasɗinawan da za a saki a yanzu sun haɗa da waɗanda suka yi kisa, wasu daga cikinsu ma suna fuskantar hukuncin sama da shekara 15 a gidan yari.
Isra'ila ta dage cewa ba za ta saki ko da mutum ɗaya ba daga cikin mutanen da ke da hannu a hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba.
An dai cimma yarjejeniyar tsagaitar wutar ne bayan shafe watanni ana tattaunawa tsakanin Hamas da Isra'ila, bisa jagorancin Amurka da Qatar da kuma Masar.
Yarjejeniyar ta ƙunshi matakai uku inda za a fara aiwatar da mataki na biyu cikin makwanni shida bayan ƙulla yarjejeniyar.
Aƙalla Falasɗinawa dubu ɗaya da 900 ne za a saki a matakin farko domin musayar Isra'ilawa 33.
Dakarun Isra'ila ma za su fara janyewa daga Gaza sannan dubban al'ummar yankin da suka ɗaiɗaita za su samu damar komawa gidajensu da suka tsere ko kuma aka tilasta masu ficewa.
Ana fatan yarjejeniyar za ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza. Har yanzu Isra'ilawa cassa'in da ɗaya da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoban 2023 na tsare a Gaza. Isra'ila na tunanin akwai Hamsin da bakwai cikinsu da suke raye. Wasu guda uku da suke raye – suna tsare tsawon shekara 10 ko ma fiye.