Monza ta sake ɗaukar Nesta wata bakwai bayan ta kore shi

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Monza ta sake ɗaukar Alessandro Nesta a matakin kociyanta wata bakwai tsakani, bayan da ta kore shi daga aikin.
Monza ta maye gurbin tsohon wanda ya tsare bayan tawagar Italiya da koci, Salvatore Bocchetti cikin watan Disamba.
To sai dai ta sallami tsohon wanda ya horar da Hellas Verona ranar Lahadi, bayan da Lazio ta doke ta 5-1 a gasar Serie A.
Hakan ya sa Monza ta ci gaba da zama ta karshen teburi da maki 13 da tazarar maki bakwai tsakani da Pama ta 18 ɗin teburi.
Bocchetti, mai shekara 38, ya ci wasa ɗaya aka doke shi shida daga karawa bakwai da ya ja ragama.
Tun farko Monza ta naɗa Nesta kociyanta a cikin watan Yuli, yayin da tsohon wanda ya tsare bayan AC Milan ya fara aikin horar da tamaula a lokacin.
Wasa ɗaya ya ci daga 17 da ya ja ragama daga nan Monza ta kore shi, yanzu kuma ta kara ɗaukan shi - zai fuskanci Lecce ranar Lahadi 16 ga watan Fabrairu a Serie A.







