''Gina United shi ne mafi mahimmaci fiye da lashe Europa''

Asalin hoton, Getty Images
Ruben Amorim ya ce gina Manchester United ta koma kan ganiya, shi ne mafi mahimmaci fiye da lashe Europa League.
Ranar Alhamis United za ta je gidan Real Sociedad a wasan farko zagayen ƴan 16 a gasar zakarun Turai.
United tana mataki na 14 a teburin Premier, an yi waje da ita a FA da Carabao Cup, kenan Europa League ne kofin da take fatan ɗauka a kakar nan.
United ce mai rike da FA Cup, wanda ta lashe a bara da ya ba ta damar shiga gasar zakarun Turai ta bana, amma Fulham ta yi waje da ita ranar Lahadi.
Fulham ta kai zagayen kwata fainal a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 har da karin lokaci.
''Hakika an fitar da mu a FA Cup, wasu da yawa na duba rawar da za mu taka a Europa, kofin da muke fatan lashewa,'' in ji Amorim
Erik ten Hag ya ɗaga kofi biyu a aikin da ya gudanar a United, wanda ya lashe FA Cup a bara, sakamakon nasara a kan Manchester City.
Kafin nan ɗan kasar Netherlands ya ɗauki Carabao Cup a 2023, bayan doke Newcastle United.
Burin Manchester United shi ne ta lashe Premier League nan da 2028 kafin bikin cika shekara 20 da kafa ƙungiyar.
United ta yi hasarar kuɗi kaka uku a jere, sannan ta rage ma'aikata 250, kuma za ta kori 200 nan gaba.









