Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Lampard zai fitar da Real a Champions League?
Chelsea za ta karbi bakuncin Chelsea a wasa na biyu zagayen quarter finals a Champions League ranar Talata a Stamford Bridge.
Ranar 12 ga watan Afirilu Real ta doke Chelsea 2-0 a wasan farko a quarter finals a Champions League a Santiago Bernabeu.
Chelsea ta yi rashin nasara a fafatawar karkashin Frank Lampard, wanda ya maye gurbin Graham Potter, bayan da ya kasa kokari a kungiyar.
Karo uku a jere Lamfard na shan kashi a jere a wasa a uku, tun bayan da ya karbi kungiyar a matakin rikon kwarya, bayan shekara biyu da ta kore shi.
Lampard ya yi rashin nasara a hannun Wolverhampton a wasan farko da ya ja ragama a rikon kwarya a gasar Premier League.
Ya kuma sha kashi a gidan Real Madrid, sannan Brighton ta ci Chelsea 2-1 a Premier League ranar Asabar wasan mako na 31.
Tsohon dan wasan Chelsea ya horar da kungiyar a karon farko tsakanin Yulin 2019 zuwa Janairun 2021, wanda Thomas Tuchel ya maye gurbinsa.
Lampard - wanda shine kan gaba a ci wa kungiyar kwallaye a lokacin da ya buga wa Chelsea tamaula - ya ci wasa 44 daga 84 a matakin koci.
Real ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Liverpool da cin 6-2 gida da waje a kakar bana.
Ita kuwa Chelsea ta yi nasarar yin waje da Borussia Dortmund da cin 2-1 gida da waje.
Kungiyar Stamford Bridge, wadda ta kai daf da na kusa da na karshe bayan cin Dortmund ta kuma kara da Inter Milan da Dynamo Zagreb a cikin rukuni.
Real Madrid wadda ta ja ragamar rukuni na shida da maki 13 ta fafata da RB Leipzig da Shakhtar Donetsk da kuma Celtic Glasgow.
Real tana mataki na biyu a teburin La Liga, ita kuwa Chelsea tana ta 11 a kasan teburin babbbar gasar tamaula ta Ingila.
Real ce mai rike da kofin bara na 14 jimilla, ita kuwa Chelsea tana da Champions League biyu.
Wasa tsakanin Real Madrid da Chelsea
2022/23 Champions League
- Real Madrid 2 - 0 Chelsea
2021/2022 Champions League
- Real Madrid 2 - 3 Chelsea
- Chelsea 1 - 3 Real Madrid
2020/2021 Champions League
- Chelsea 2 - 0 Real Madrid
- Real Madrid 1 - 1 Chelsea
1998/1999 European Super Cup
- Chelsea 1 - 0 Real Madrid
1970/1971 Euro Cup Winners Cup
- Chelsea 2 - 1 Real Madrid
- Chelsea 1 - 1 Real Madrid
Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan Real da ya je da su Stamford Bridge buga wasa na biyu ranar Talata.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. da kuma Rüdiger.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.