Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benzema zai buga Champions League na 150 a gidan Chelsea
Chelsea za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu zagayen quarter finals a Champions League ranar Talata a Stamford Bridge.
Sun kara a wasan farko a bana a gasar zakarun Turai ranar 12 ga watan Afirilu a Santiago Bernabeu, inda Real ta ci 2-0.
Dan wasan tawagar Faransa shine ya ci kwallon farko a wasa na 149 da ya yi a Champions League.
Ranar Talata yana daga cikin 'yan kwallon da Real ta je da su Ingila, domin buga karawa ta biyu, wasa na 150 da zai yi kenan a Champions League.
Kenan zai zama na shida a jerin wadanda suka yi karawa 150 a gasar ta Champions League.
Cristiano Ronaldo ne kan gaba mai wasa 186 a Champions League ciki har da karawar da ya yi wa Manchester United da Real Madrid da Juventus.
Ryan Giggs shine yake da tarihin buga wa kungiya daya, Manchester United karawa 151 a Champions League.
Cikin wasa 149 da Benzema ya yi a Champions League ya ci kwallo 90 da daukar kofin karo biyar tun daga kakar 2013/14.
Ya fara buga wa Real Madrid gasar a 2009-10. Tun daga lokacin ya ci kwallo a kowacce kakar tamaula idan ya buga, in banda 2012/13 da ya yi jinya.
Kakar 2021/22 ta Cjampions League ita ce da yafi taka rawar gani da cin kwallo 15 a fafata 12.
Jerin 'yan wasan da suka buga Champions League 150:
1. Cristiano Ronaldo 186
2. Casillas 181
3. Messi 163
4. Xavi Hernández 157
5. Man United 151