Waiwaye: Ƙara wa'adin biyan kuɗin aikin Hajjin bana da soke karɓar digirin jami'o'in Benin da Togo

An wallafa

Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Ina sane da duk guna-guninku game da matsin rayuwa - Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin gina ƙasa da za ta tabbatar da daidaito da adalci da kuma rage giɓin da ke tsakanin al'umma.

Ya ce ko da yake ya yi imani masu kuɗi su ci moriyar dukiyar da suka mallaka da guminsu, amma jazaman ne duk wani ɗan Najeriya mai aiki tuƙuru ya samu damar da zai ci gaba a rayuwa.

Shugaba Tinubu na wannan bayani ne a cikin jawabin da ya gabatar na shiga sabuwar shekara ta 2024.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki ba kama hannun yaro don tabbatar da ganin duk 'yan Najeriya sun ɗanɗani daɗin gwamnatinsu.

Tinubu ya ce abin murna sosai yi wa al'ummar ƙasar maraba da shiga sabuwar shekara ta 2024, kuma dole ne su ɗaga hannu don yi wa Allah godiya da wannan karimci da baiwa da ya yi wa Najeriya da kuma rayukan al'ummarta.

Ya ce a tsawon wata bakwai da ya shafe a kan mulki, ya ɗauki wasu matakai da suka wajaba kuma masu wahala don ceto ƙasar daga shiga bala'in tattalin arziƙi, daga ciki akwai batun cire tallafin man fetur da dunƙule tsarin canza kuɗaɗen ƙasashen waje, da ke amfanar masu kuɗi kawai

Shugaba Tinubu ya ce yana sane da cewa a lokuta da dama hirarraki da muhawarorin jama'ar Najeriya na mayar da hankali ne a kan batutuwan tsadar rayuwa da matsanancin hauhawar farashi wanda a yanzu ya kai kashi 28% da kuma yawan marasa aikin da ba za a amince da shi ba.

Hukumar Alhazan Najeriya ta ƙara wa'adin biyan kuɗin aikin Hajjin 2024

Hukumar Alhazan Najeriya ta tsawaita wa'adin biyan kuɗin aikin Hajji na 2024.

Cikin wata sanarwa a ranar Talata, jami'ar yaɗa labarai Fatima Sanda Usara ta ce yanzu wa'adin ya koma 31 ga watan Janairun 2024.

Tun da farko hukumar ta haƙiƙance cewa za ta rufe karɓar kuɗin daga ranar 31 ga watan Disamba na 2023 duk da ƙarancin mutanen da aka samu.

"An ɗauki matakin ne saboda ƙorafin da malaman addini suka yi, da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, da gwamnoni, da kuma sauran masu ruwa da tsaki," in ji sanarwar.

Hukumar ta bayyana naira miliyan 4.5 a matsayin kuɗin aikin Hajjin na bana, farashi mafi tsada ke nan a tarihi.

Tinubu ya sa hannu a kan kasafin kuɗin 2024

Shugaba Bola Tinubu ya sa hannu kan ƙudurin kasafin kuɗin bana na sama da naira tirliyan 28 zuwa doka.

Ya dai bai wa al'ummar Najeriya tabbacin cewa zai bi diddigi wajen ganin yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin, ya kuma ce ya umarci dukkan ma'aikatu da hukumomi su riƙa bayar da rahoton yadda suke aiwatar da kasafin kuɗin wata-wata ga ma'aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya fitar ta ce manyan ɓangarorin da kasafin kuɗin ya mayar da hankali a kansu akwai tsaron ƙasa da samar da tsaro a cikin gida, samar da aikin yi da daidaita harkokin tattalin arziƙi da bunƙasa yanayin zuba jari da rage talauci.

Shugaba Tinubu ya nanata cewa ƙudurinsa na kyautata harkokin zuba jari da ƙoƙarin samar da al'umma mai bin doka wadda ba za ta fifita kowanne mutum ba, zai fara da muhimman sauye-sauye a ɓangaren shari'a, wanda kuma an samar da kuɗaɗen yin su a cikin kasafin kuɗin.

"Samar da kuɗi ga ɓangaren shari'a wani muhimmin ƙuduri ga ƙoƙarinmu wajen tabbatar da wata al'umma mai bin doka da tsayawa a kan daidai. An ƙara kuɗaɗen da ake warewa ɓangaren shari'a daga tushe daga naira biliyan 165 zuwa naira biliyan 342," cewar shugaban ƙasar.

Sanarwar ta ce muhimman alƙaluma a cikin kasafin kuɗin su ne manyan ayyuka naira tirliyan goma da ayyukan yau da kullum naira tirliyan 8.8 sai biyan basuka tirliyan naira 8.2 sai kason tallafi na doka daga asusun tarayya naira tirliyan 1.7.

Najeriya ta soke karɓar digirin jami'o'in Benin da Togo

Najeriya ta ce ta ɗauki matakin dakatar da tantance shaidar karatun digiri daga jami'o'in Jamhuriyar Benin da na Togo.

Matakin ya zo ne bayan wani binciken ƙwaƙwaf da jaridar Daily Nigerian ta yi a baya-bayan nan, inda ta ce wakilinta da ya ɓad-da-kama, kuma ya samu takardar shaidar digiri daga wata jami'a a Jamhuriyar Benin a cikin mako shida kacal.

Mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ta Najeriya, Augustina Obilor-Duru cikin wata sanarwa da ta fitar, na cewa rahoton ya bayyana hanyoyin da wasu ƴan Najeriya ke bi domin samun takardar shaidar karatun digiri da nufin samun damamrmakin aiki da ba su cancanta ba.

"Ma'aikatar ilimi ta koka da irin wannan ɗabi'a kuma daga ranar 2 ga watan Janairun 2024, ta dakatar da tantance takardun shaidar karatun digiri daga Benin da Togo har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

"Binciken dai zai haɗar da ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya da kuma ƙasashen biyu da ma'aikatun da ke kula da ilimi a ƙasashen da kuma hukumar tsaro ta farin kaya da hukumar kula da shirin matasa 'yan hidimar ƙasa, NYSC."

Ma'aikatar ta yi kira ga yan Najeriya su ba da gudunmawa wajen samar da bayanan da za su taimaka wa kwamitin yayin da yake neman hanyoyin magance faruwar haka a gaba.

Ma'aikatar ta kuma yi bayani kan ƙalubalen da take fuskanta game da matsalar bara-gurbin makarantun ƙetare ko a cikin gida waɗanda mutanen da ba su ji ba su gani ba, ke faɗawa tarkonsu ko kuma wasu ƴan Najeriya waɗanda da saninsu suke karatu a makarantun.

Jaririn da aka fara haifa a asibitin ƙasa na Najeriya a 2024

Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga mata masu juna biyu su ɗauki zuwa asibiti domin duba lafiyarsu da muhimmanci, da yin gwajin cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV.

Sanata Remi ta ce wannna zai bai wa jami'an lafiya damar bin hanyoyin kare jaririn da ke cikin uwa daga kamuwa da cutar, da tabbatar da ingancin lafiyar uwa da jaririnta.

Misis Remi ta bayyana hakan ne a wata ziyara da ta kai Babban asibitin gwamnatin Tarayya da ke Abuja, inda ta tarbi jaririn farko da aka haifa a wannan sabuwar shekarar ta 2024.

Ta kuma yi kira ga masu hannu da shuni su shiga a dama da su wajen taimakawa gwamnati na cika burin samar da ingantaccen fannin lafiya ga 'yan Najeriya baki ɗaya.

Hisba ta kama babbar mota maƙare da dubban kwalaben giya a Kano

Hukumar Hisba a jihar Kano ta ce ta kama wata babbar mota maƙare da kwalaben barasa sama da 24,000.

Daraktan gudanarwar hukumar, Alhaji Abba Sufi ne ya bayyana haka ranar Laraba lokacin da yake duba motar da jami'ansa suka kama cikin dare a kan titin zuwa Zaria.

Mallam Abba Sufi ya ce jami'an Hisba suna aiki tuƙuru wajen yaƙar masu safarar miyagun ƙwayoyi da barasa zuwa jihar ta iyakokin ƙasashe maƙwabta.

Ya kuma yaba wa jami'an hukumar kan yadda suke haɗa kai da masu ruwa da tsaki wajen yakar masu safarar giya a Kano bisa tsarin shari'a.

A nasa jawabin, wani jami'in hukumar Fu'ad Ɗorayi ya ce an kama matuƙin babbar motar da ƙarin mutum biyu.

Hukumar Hisba ta Kano ta saba kamawa da fasa kwalaben giya a jihar, saboda a cewarta safara da kuma shan barasa sun saɓa wa koyarwar Musulunci.

NNPCL ta tabbatar mana ba za a ƙara kuɗin man fetur ba a Najeriya- IPMAN

Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, IPMAN ta ce babu kanshin gaskiya dangane da rahotanni da ke yawo cewa za a kara kudin man fetur.

Shugaban ƙungiyar na arewacin najeriya, Alhaji Bashir Ɗan Malam, a wata hira da BBC ya ce sun samu tabbaci daga kamfanin mai na kasar mai zaman kansa wato NNPCL.

Dama dai kamfanin NNPCL ya musanta rahotannin cewa ana shirin kara farashin litar man fetur a kasar.

A cewar NNPCL mutane su kwantar da hankalinsu, Najeriya ba za ta kara kudin mai ba a wannan lokacin.

Tuni dai aka fara ganin dogayen layin ababan hawa a gidajen mai musamman a biranen Abuja da Legas da karin wasu a sassan Najeriya.

Ana sayar da litar mai a Najeriya tsakanin naira 650 zuwa 660.

Sai dai a watan Disambar 2023 ne bankin duniya ya shawarci Najeriya da ta kara kudin man zuwa naira 750, idan dai har kasar na son daina biyan tallafin man kocakan.b