Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda mata ke fama da wariya a wurin aiki
''Kasancewata mace ina ayyuka da dama da suka zama kamar al'ada a wurina wadanda ba ma a maganar wai a gode min don na yi su," in ji Maria daga Argentina, take bayani lokacin da aka nemi ta yi bayani kan yadda aikinta yake a ofis.
''Wani lokaci sai na ji ni kamar uwa, wani lokacin kuma na ji kamar wata matar aure da ba ta da kima."
Matar mai shekara 30, wadda ta nemi a boye sunanta na gaskiya ta fara aiki ne tun tana 'yar shekara goma sha.
A lokacin tana shekara 19 ta samu aiki a matsayin sakatariyar wani dan siyasa.
Aikin nata ya kunshi aikin ofis da amsa waya da kuma shirya ganawar baki.
Amma kuma ta ce duk da haka aikin da take yi a kullum har zuwa yau duk da kara mata matsayi da aka yi, ya hada har da hada shayi da gahawa da dumama abinci da zuba wa shugaban nata abinci da kuma wanke kofi da kwanuka.
Ta koka da cewa "A lokacin bikin zagayowar ranar haihuwar matarsa ma sai da ya sa na sayo mata furanni na taya murna saboda aiki ya yi masa yawa.''
Ba Maria ce kadai a cikin irin wannan yanayi na wurin aiki ba.
A Amurka mata sun fi samun kansu a yanayi na aikin da ba za a kara musu girma ba a wurin aiki, in ji Lise Vesterlund.
Marubuciya kuma malama a fannin tattalin arziki a Jami'ar Pittsburgh.
Kuma kamar yadda wani rahoton Bankin Duniya ya nuna duk da cewa mata ne kashi 39 cikin dari na yawan ma'aikatan duniya a 2021, 'yan kalilan ne daga cikinsu ke kaiwa matsayin shugabanci.
Mujallar Forbes ta ce a 2021 kusan kashi takwas ne kawai na manyan kamfanonin duniya 500 mata ke shugabanta.
To a nan mun ji ta bakin wasu mata a sassan duniya a kan wannan yanayi na aiki.
Tare da ba su shawara kamn yadda za su ki yarda da irin wadannan ayyukan da ba a samun karin girma, wadanda masu nuna bambanci tsakanin maza da mata ke dangantawa da aikin mata.
Ki ki goge ofis! Ai ba zai yiwu ba
Wasu daga cikin irin wadannan ayyuka da ba a kara wa mutum girma, suna iya kasancewa na kaskanci in ji Rafat Salami, daga Najeriya.
''Lokacin da na samu aikina na farko a matsayin 'yar jarida, na cika da murna.
Na dauka cewa dama ta samu gareni na kawo sauyi a yadda wasu al'amura suke gudana.
To amma sai na ga kawai na fara aikin da goge tebur da sauran kayayyaki na ofis.''
Ita dai Rafat 'yar jarida ce da ke aiki a Abuja da ke aiki da gidan rediyon Muryar Najeriya (Voice of Nigeria).
kafin ta samu wannan aiki na gwamnati ta yi ayyuka a kamfanoni da yawa da ta ce ana sa ta ayyukan da ba su ma shafi fannin aikin ofis ba.
Rafat ita ce karama cikin mata biyu da ke aiki a matsayin wakilai masu hada rahoto a gidan rediyon da take aiki.
A cikin ayyukan da take yi sai aka hada mata har da cewa ita ce za ta rika tsaftace ofishin.
''Sai na gyara na kuma tsaftace gidana kafin na tafi wurin aiki, kuma idan na je wurin aikin abu na farko da zan fara da shi shi ne na goge ofis din,'' in ji ta.
Amma Rafat ta tashi tsaye ta nemi 'yancin kanta inda ta gaya wa shugabannin wurin cewa su samo mai goge ofis kawai.
''Na gaya wa kaina cewa, 'Kai ba za ta sabu ba, ba zan yi ba'. Daga nan na fara kin yin aikin. Suka kasa sanin dalilin da ya sa na yi haka.
Rafat ta ce wannan mataki da ta dauka ya ba abokan aikinta mamaki . Daga karshe dai ta bar aikin.
''Idan mace ta ki yarda ta yi wani aiki sai a ce mata tana da girman kai. Shi ya sa kika ki samun miji,'' in ji ta.
Ta ce "A gida ki kula da mijinki da kuma 'ya'yanki, kuma idan kika je wurin aiki kowa yana sa ran ya ga kin kula da sauran maza abokan aikinki.
Wannan ya sa wani lokaci sai ki daga kafa ki ce ba kya so a dauke ki mai tsaurin kai.''
Rafat ta ce abu ne mai wuya mace ta iya kaucewa daga wasu ayyuka da ake dauka na mata ne kawai, a wasu wuraren, saboda haka ne a wani lokacin har take dafa wa mutane abinci.
To amma ta ce a wurin aiki yana da kyau ka ki yarda da yin irin wadannan ayyuka, wanda abin ta yi kenan a yanzu.
Ta ce: ''Ni na san kaina ina mutunta kaina. Kuma ba na sassautawa a kan duk abin da zai keta min haddi. Ina tsayawa a kan ra'ayina. Kuma ana mutunta ni a kan haka.''
Yin shayi da gahawa
Ita ma Nana Watarai daga Japan, kusan labarinta iri daya ne da na Rafat.
Ta ce, "Mahaifiyata tana aiki a wani babban kamfanin abinci. A lokacinta, abokanan aikinyta maza sai kawai su rika sa mata su yi musu shayi ko gahawa. Abu ne da aka dauka ba wata matsala ba ne, ya zama kamar wata al'ada kawai,'' in ji Nana.
Kowa a ofishin yana da kofinsa, kuma ana sa ran matan ofishin su san kofin kowa.
Sannan kuma bayan aikinsu na ofis na kullum, su rika yi da zuba wa kowa shayi.
"Mahaifiyata da sauran abokan aikinta mata a ofishin suna karba-karba a aikin dafawa da kuma raba shafin da safe.
Har ma abin ya zama kamar wani aikinsu na kullum. Shi ne aikinsu na farko a duk safiya.
Nana ta koyi darasi daga abubuwan da mahaifiyarta ta ba ta labari na game da rayuwarta a wurin aiki.
Wannan ya sa take neman manyan mukamai a wurin aiki.
Lokacin da ta fara aiki kusan shekara 30 da ta wuce, ta lura cewa ana mayar da mata kamar yadda ta ce baya a dangi, inda ake ware musu wasu ayyuka.
Ta ce: "Maza suna samun mukamai da suka fi kima da muhimmanci, kamar bangaren sayar da kaya da shugabanci da tallata kaya da sauransu.
Su kuwa mata ana ba su ayyuka ne kamar mataimaka a ofis da sauran wasu kananan ayyuka kusan na taimaka wa maza.
A yawancin kamfanoni babu mata daraktoci ko manyan shugabanni.''
Wannan ne ya sa ta yanke shawarar yin aikin wucin-gadi a matsayin mai shirya wurin taro da kuma mai fassara jawabi wato tafinta.
Kuma ta ce ta kura da batun yin iyali domin ta samu ta mayar da hankali a kan aikinta.
Nana ta ce akwai bukatar lalle a samu sauyi kodayake ta yarda cewa an samu sauyi idan aka kwatanta da zamanin mahaifiyarta.
Misali gwamnatin Japan ta yi wata doka a 1986, wadda ta tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata wajen samun aiki da karin girma da sauransu.
Nana na fatan a dalilin irin wannan doka da aka yi a Japan nan gaba ba zai zama cewa mace sai dai ta zaba tsakanin rayuwar aiki ko kuma ta yin iyali ba.
Ana bukatar karni biyu kafin a daidaita bambancin
Wani sabon rahoto da aka yi ya nuna cewa ana bukatar shekara 132 daga yanzu kafin a samar da cikakken daidaito na aiki a tsakanin maza da mata.
Rahoton wanda taron duniya kan tattalin arziki ya fitar a watan Yuli na 2022 ya ce tsadar rayuwa na taimakawa wajen kara wannan bambanci, kuma tana tasiri ne a kan mata.
Inda bambancin ya fi girma a duniya shi ne yankin kasasshen Kudancin Asia, inda rahoton ya ce za a dauki karni biyu kafin a rufe gibin.
Rahoton ya ce annobar korona ta sake mayar da al'amarin baya sosai.
Lise Vesterlund, malama a fannin tattalin arziki a Jami'ar Pittsburgh tana ganin gibin zai ci gaba da kara girma ne idan mata suka ci gaba da yarda suna yin ayyukan da ake danganatawa na gida, a ofis (kamar wanke-wanke da dafa shayi da tsaftace wuri da sauransu).
Malamar ta hada kai da wasu abokanta uku, suka rubuta littafi (mai suna The No Club: Putting a Stop to Women's Dead-End Work), wanda ke nuna wa mata yadda za su bijire wa yin wasu ayyuka da ake dangantawa da dama a duniya.
Misalan ayyukan gida da ake yi a ofis
Wadannan matan sun bayyana wa sashen Mundo na BBC, irin yadda suka samu kansu a wannan matsala.
Edith daga Mexico: "Shugaban wurin aikina ya sa na hada masa lokacin da zai je ya sabunta lasisinsa na tukin mota. Sai na kai kara sashen kula da ma'aikata.
Mako uku da yin haka sai aka kore ni daga aiki, da cewa wai ban san yadda zan girmama shugaba ba da kuma aiki da jama'a.''
Gabriella a Argentina:
Ta ce: ''Aikin sakatariya a kamfanonin lauyoyi da dama ya hada da dafa shayi da gahawa da siyo abincin rana da gyara tebur bayan an ci abinci da wanke kwanuka da kofuna da makamantansu. Kuma abin takaicin a dan albashi maras yawa.''
Silvia (ba sunanta na gaskiya ba ne) daga Chile:
"Ina aiki a wani babban kamfanin lemon kwalba, wata rana sai shugaban wurin ya kawo mana kek (cincin) mu raba.
A lokacin yawan maza ya ninka na mata kusan hudu.
Duk da haka shugaban ya ce in yanka kek din na raba. Sai kawai na ji daban, na tsaya kikam."
Ga yadda za ki yi tirjiya ki tsira
Maria, wadda ke aikin sakatariya da muka ba da labarinta a baya, wadda take yi wa shugabanta a ofis ayyuka hatta irin na gida a wurin aikin, tana jin takaici da kunya a irin halin da take ciki na aikin.
Ta ce "Mun san juna tsawon lokaci, yanzu abin ya zama kamar alakar mahaifi da 'ya.
Zan iya cewa ba zan yi ba ta luma ba tare da na bata rai ba, to amma ban taba ki ba. Ban san me ya sa ba,'' in ji ta.
"Na san cewa matsayina ya wuce wannan aikin. a yawancin lokaci, nakan tambayi kaina , me ya sa nake yin aikin nan?''
Lise ta yarada cewa ba abu ne mai sauki ba ka ce a'a ba za ka yi ba, amma ta shawarci mata da su yi magana a tattauna domin samun maslaha.
Ta ce "maimakon kawai ki ce to, ki ce : To zan yi wannan aikin, amma kuma fa zai iya shafar ainahin aikin da ya kamata na yi na ofis din.'' da dai sauran kalamai irin wadannan.
Ta kara da cewa, ''Ki danganta lamarin da ci gaban harkar kasuwancin kamfanin ki ce ''a karshe fa harkar kamfanin za ta iya samun nakasu.''
Ta ce za a iya samun sauyi ne idan shugabannin wurin aiki suka san cewa ba wa mata karin aikin da bai kamata ba ka iya shafar ainahin aikin wurin.
Maria, wadda ke karatunta na digiri na uku (digirin digirgir, PhD), tana shirin barin aikin da take yi yanzu, amma ta lashi takobin cewa ba za ta yi ba a nan ba a duk wani aiki da ta samu nan gaba.
Rafat daga Najeriya ta gaya wa BBC, cewa kodayake mata ba su da dama sosai ta neman yin yarjejeniya a wurare da dama kamar yadda al'ada ta saba.
To amma ta yarda cewa wani lokaci mutum ya toge ya ki yarda, hakan na tasiri, inda ta bayar da misalin abin da ta yi a lokacin tana aikin wucin-gadi
Ta ce: "Ni kadai ce mace a wurin taro, kuma na fi kowa kwarewa a wurin. Amma duk da haka aka ce wai na rika rubuta abin da ake tattaunawa a taron. Kawai sai na tashi ke da keke na gaya musu cewa su nemi sakatare da zai yi musu wannan aikin.''