Barca ta kusa daukar Alonso, akwai yiwuwar Chelsea za ta kure lalitarta

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona na ci gaba da tattaunawa da Chelsea kan dan wasan baya na Sifaniya Marcos Alonso, kuma tana da yakinin cewa za ta cimma nasarar daukan dan wasan mai shekara 31. (90min)
Alonso ya riga ya yi sallama da jami’an Chelsea a filin da kungiyar ke atisaye na Cobham, yayin da yake sa ran kammala batun tafiyar tasa a cikin karshen mako. (Mail)
Crystal Palace na son dawo da dan wasan baya na Ingila Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 24, daga Manchester United. (Sky Sports)
Everton na shirin doke West Ham a kokarinta na dauko dan wasan tsakiya na Belgium Amadou Onana, mai shekara 20 daga Lille. (Mirror)
Da yiwuwar Chelsea za ta karya tarihin sayen dan wasan baya mafi tsada, wanda a yanzu Harry Maguire ke rike da shi (£80m ), a kokarinta na dauko dan wasan baya na Faransa, Wesley Fofana, mai shekara 21 daga kungiyar Leicester City. (Telegraph)
Tottenham na Shirin cimma yarjejeniya da Udinese domin daukar dan wasan baya na Italiya Destiny Udogie, a cikin mako mai shigowa. (Fabrizio Romano)
Dan wasan tsakiya na Barcelona, dan asalin Netherlands, Frenkie de Jong, mai shekara 25, na shirin share wuri domin ci gaba da zama a kungiyar mai buga wasa a Sifaniya, tare da cewa za a rage masa albashi. Duk kuwa da kwadayin da kungiyoyin Chelsea da Manchester United suka nuna na daukar sa. (Sport - in Spanish)
Leeds na kokarin ganin ta dauko dan wasan gaba Arnaud Kalimuendo, dan asalin kasar Faransa, daga Paris St-Germain kan kudi £22m. (Sun)
Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Manchester United da Red Bull Salzburg kan yiwuwar sayen Benjamin Sesko, mai shekara 19, dan asalin Slovenian. (Sky Sports)
Middlesbrough na kammala yarjejeniyar daukar dan wasan gaba na Amurka, mai shekara 21, Matthew Hoppe, daga kungiyar Mallorca. (90min)
Tsohon dan wasan tsakiya na Barcelona, Cesc Fabregas ya bukaci Lionel Messi, ya baro Paris St-Germain domin komawa Nou Camp. (Mirror)










