Kocin Man Utd na kaunar ganin Cristiano Ronaldo a kungiyar

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ronaldo ne ya fi ci wa Man Utd kwallo a gasar Premier da Zakarun Turai a bara
An wallafa

Kociyan Manchester United Erik ten Hag ya ce yana matukar farin cikin ganin Cristiano Ronaldo a cikin tawagarsa.

Ana ta maganganu iri-iri a kan Ronaldo, mai shekara 37, a bazaran nan yadda ake ganin yana cike da burin yin wasa a wata kungiya da ta samu gurbin gasar Zakarun Turai.

Kasancewar Anthony Martial ba zai yi wasan Lahadi da United za ta yi da Brighton ba saboda raunin da ya ji, kila Ten Hag zai bukaci dan wasan na Portugal.

"Ina matukar farin ciki yana nan tare da mu," in ji Ten Hag.

"Muna da gwarzon dan gaba. Za mu bi tsarin da muka yi."

Ten Hag ya kara maimaita kalaman da ya yi ga wata kafar yada labarai ta Holland a makon nan inda ya ce 'yan wasan kungiyar ciki har da Ronaldo da suka fice a wasan sada zumunta da ta yi Lahadin da ta wuce da Rayo Vallecano a Old Trafford kafin a tashi daga wasan ba su yi abin da ya dace ba.

Tsohon kociyan na Ajax ya ce kungiyar ta Old Trafford har yanzu tana neman sabbin 'yan wasa a bazaran nan.

Sai dai ya ce ba wai kowa ne dan wasa suke nema ba, wanda ya cancanta suke bukata.