'Yadda na jefa kaina cikin katutun bashi wajen neman taimakon malamai'

Evarline Okello

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Evarline Okello ta fashe da kuka a yayin da take bayyana mani katutun bashin da yake kanta na ɗaruruwan daloli bayan da ta biya wani pasto kuɗi domin ya yi mata addu'a.

Tana zaune ne a wata ƙaramar bukka a Kibera da ke Nairobi, babban birnin Kenya, ga shi kuma ba za ta iya kula da ƴaƴanta huɗu ba.

Ms Okello ta shafe watanni kuɗi ba su shiga hannunta ba, ta faɗa mani yayin da muke tattaunawa ta wayar tarho. Lokacin da ta samu labarin pasto ɗin da addu'oinsa ke zama karfiyan, sai ta ji tana son ganinsa. Ya buƙaci ta bashi $115 kwatankwacin £96.

Hakan yana nufin bayar da sadaka da nufin samun biyan buƙata kan wani al'amari.

Ms Okello ta ranci kuɗi daga wajen ƙawarta, wadda ta karɓi bashi a madadinta. An faɗa mata cewa addu'oin pasto ɗin suna da tasiri sosai ta yadda cikin mako guda za ta mayar da kuɗinta.

Sai dai hakan ba ta tabbata ba. A maimakon haka ma, lamura ne suka yi muni, in ji ta. Bashin da ƙawarta ta karɓa ya sake taruwa saboda rashin biyan ribar ta da ta hau kai. A yanzu ana binta fiye da $300 kuma ba ta ma san yadda za ta biya kudin ba. Ƙawarta ta daina yi mata magana kuma har yanzu ba ta aiki.

"Abubuwa sun dagule mata, na yanke ƙauna," in ji ta.

'Neman mafita daga malamai'

Kenya ta fuskanci matsalar tsadar kayan masarufi. Farashin abinci ya ƙaru da kusan kashi 16 cikin 100 cikin shekara ɗaya kafin Satumban 2022, a cewar hukumar ƙididdiga ta Kenya yayin da alƙaluma daga Bankin Duniya suka nuna adadin ƴan Kenya da suka rasa aikinsu ya ninka sau biyu cikin shekara bakwai da ta gabata.

"Mutane na zaune cikin ƙunci," in ji Dr Gladys Nyachieo, wata malama a jami'ar Multimedia University da ke Kenya.

Hoton wani ɗan Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi ta gudanar da zanga-zanga a Kenya saboda tsadar rayuwa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan ya sanya su neman taimakon malamai, in ji ta kuma mutane da dama a yanzu suna son su biya domin neman agajin bokaye da malamai ko da ya zama sai sun yi rancen kuɗi.

"Ana faɗa wa mutane cewa Ubangiji ba ya son su kasance cikin talauci. Don haka sai su bayar da sadaka," kamar yadda ta faɗa mani.

Wannan tsarin ya samo asali ne daga abin da ake kira "Prosperity Gopel" wanda ke nufin Ubangiji na yalwata arziki da lafiyar masu tsoron sa. Ana karfafa wa masu ibada gwiwar su yi imani ta hanyar bayar da kuɗi da ake iƙirarin za su samu ninkin abin da suka bayar.

"Prosperity Gospel" ya samo asali ne daga Amurka inda ya samu karɓuwa a farkon ƙarni na 20. Zuwa ƙarshen shekarun 1970 da farkon shekarun 1980, pastocin Najeriya suna zuwa Amurka domin ƙaro sani game da tsarin kuma a farkon shekarun 2000, tsarin ya ƙara samun karɓuwa a sassan Afirka wanda aka samu Amurkawa masu shigar da mutane addinin kirista kamar Reinhard Bonnke wanda ya tattaro jama'a daga Legas zuwa Nairobi. Abin na ci gaba da samun karɓuwa har zuwa yanzu.

Hoton masu ibada a coci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Evangelist Reinhard Bonnke wanda ya mutu a 2019, ya shahara sosai a Nigeria

Dr Nyachieo ta kuma ce wani abu da ke kwaɗaitar da mutane neman bashi - saƙonnin tayin rance da ake hankaɗowa ƴan Kenya ta wayoyinsu na hannu. "Mutane suna nema kuma su samu kuɗin," in ji ta.

Abin da ke nan ya faru da Dennis Opili ɗan shekara 26. Zuciyarsu ta karaya bayan shafe fiye da shekara uku yana neman aiki, ya tambayi abokinsa yadda zai samu taimako.

"Ya bani shawarar cewa akwai wani coci da za ka je a yi maka addu'a. Za ka bayar da sadaka, sai a yi maka addu'a, sai kuma ka samu aiki," in ji Mista Opili.

An fada masa ya riƙa bayar da sadaka duk ranar Lahadi tsawon wata uku, a jumulla kusan $180 ke nan.

Lokacin da ya kashe kuɗin da yake ajiyarsu, sai ya karɓi rancen kusan $120 daga manhajojin da ke bayar da tallafin kuɗi da kuma abokanai.

"Na yi imani da abin da pasto ɗin ya fada min, cewa zan samu aiki. Don haka sai na ji ba ni da matsala da yin rance, saboda na yi tunanin zan samu kudin da zan biya kuɗaɗen da ake bina."

Amma da ban samu aiki ba, sai Mr Opili ya fara shakkun cewa an yaudare shi.

Hoton Dennis Opili

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dennis Opili ya yi rance daga manhajojin bayar da rance domin biyan pasto

Nan da nan kuma kamfanonin da ya karɓi rance suka fara nemansa ya biya su.

"Wasu lokutan, sai kawai ina zaune cikin nishaɗi ina tunanin wasu abubuwan. Sai kawai wani ya kira ka, suna neman ka biya su kuɗinsu kuma ba ka da kuɗin biyansu, kamar yadda ya ce.

Na tsorata saboda ba ka san matakin da za su ɗauka ba idan ka ƙi biyansu. Ba ka sani ba ko za su iya maka ka a gaban kotu ko ma su iya kai ka hannun ƴan sanda."

A yanzu ya samu sa'ar samun wani aiki da ake biyansa abin da bai taka kara ya karya ba wanda kuma ya taimaka masa wajen biyan wani kashi na kuɗin, ga kamfanonin rance da abokanansa.

"Na yi imani da Ubangiji," in ji shi. "Abin da kawai zan yi shi ne na ƙara yin taka tsan-tsan."

Takura mutane su bayar da sadaka

Ba kawai a Kenya bane mutane ke fama da katutun bashi saboda kawai suna neman taimakon malamai. Wata mata da take zuwa wani cocin Najeriya da ke Amurka ta ce ita da mai gidanta sun fuskanci matsi kan bayar da kuɗi - har da tsammanin su bayar da sadaka.

"Sarah" kamar yadda nake kiranta, ta nemi na ɓoye sunanta da jihar da ake zaune a Kudancin Amurka, saboda tsoron barazana daga cocin ko kuma lauyoyinsa.

Ta ce masu ibada da pastocin da ke cocin da take zuwa na tsammanin ta basu sadakar kashi 10 cikin 100 na albashinta domin taimaka wa cocin da shugabancinsa a Najeriya.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana alaƙanta Evangelist Oral Roberts (1918-2009) a matsayin uban Prosperity Gospel

An ƙayyade wa jagororin al'umma wani adadi da za su riƙa bayarwa duk wata, in ji ta, wanda ya matsa lamba kan masu ibada su bayar da sadaka. An faɗa wa mambobin cocin cewa za su samu tabarraki da shugaban pastocin da ke Najeriya.

Sarah ta bayyana cewa ta ga mutane suna bayar da sadaka da katinsu na banki.

"Ina tuna wani lokaci a cocin wata mata ta ce: 'Ina ta biyan sadaka amma kamar ba ni da isasshen kuɗi a ƙarshen wata."

Martanin paston, in ji Sarah, shi ne faɗa wa mutane cewa bayar da sadaka ya fi biyan kuɗin hayarsu. Sannan ta ce duk wanda ya nuna shakku kan rashin faruwar wata mu'ujiza sai a ce masa: "Ba ka bayar da isassun kuɗi ba, ba ka bayar da sadaka wadatacciya ba. Imaninka ya yi rauni."

Ta ce an takurawa mijinta ya rabu da ita, saboda tana yawan yi masa tambayoyi - amma sai su duka biyun suka bar cocin.

Mafita ta ƙarshe

Me ya sa wasu suke ci gaba da zuwa waɗan nan majami'u?

Dr Jörg Haustein, wani farfesan addinin kirista a Jami'ar Cambridge ya ce abu ne mai yiwuwa ka fahimci dalilin da ya sa mutane ke ci gaba da bayar da sadaka bayan ba sa ganin wani ci gaba kamar yadda ake tallatawa".

Ga waɗanda ke da rufin asiri kamar waɗanda suke cocin da Sarah ke zuwa, Dr Haustein ya ce Prosperity Gospel na samar da ci gaban tattalin arziki da mutane ga kwaɗayin samu."

Amma hakan na iya jan hankalin wadanda ke fama da talauci ma, in ji shi.

"Cocin da ya ce: "Mun san kuna cikin ƙunci kuma muna da mafita mai ɗorewa gareku,' zai fi jan hankali fiye da wanda yake fatawar samar da sauyi."

Amma na tambayi saboda me mutane mutane suke ci gaba da bayarwa duk da hakan zai jefa su cikin bashi?

"Ba kamar caca ba ce a lokacin da ba ka da kuɗi? Dr Haustein ya tambaye ni.

"Wani abu ne da ake ganin za a iya biya saboda za ka iya karɓar rancen ɗaruruwan kuɗin Kenya ta waya domin zuba jari da duba ko hakan zai taimaka.

A can Kenya, Evarline Okello ta ce abin da ta fsuaknta bai sa ta watsar da imaninta ba.

"Ba zan iya cewa cocin ba shi da manufa mai kyau ba. Cocin yana da kyau. Pastocin ne suke kauce hanya. Sune suke tambayar kudi."