Gargadar da Barcelona da Xavi za su fuskanta a El-Clasico

Barcelona da ke ta daya a gasar La Liga za ta tafi Santiago Bernabeu domin buga wasan El-Clasico a ranar Lahadi, yayin da take da maki daidai da daidai da Real Madrid, sai dai kwallo daya kacal aka sanya wa kungiyar a wannan kakar.
Magoya bayan kungiyar suna yadda ta kashe yuro miliyan 145 kan sabbin 'yan kwallo, duk da cewa ta fuskanci matsalar kudi, sai dai duk mai kallon kwallon kungiyar ya san cewa kwalliya na biyan kudin sabulu a cikin filin wasa.
Wasanni shida da ta buga a La Liga ba a sa mata ko kwallo guda ba, ta buga da kungiyoyi irin su Real Valladilid da Cadiz da Elche da kuma Real Mallorca - wadanda dukansu ba a sansu da yawan cin kwallaye ba.
Amma alkaluman da ake da su sun nuna yadda mai tsaron ragar Barcelona Marc-Andre ter Stegen ya rika buge kwallaye da ake kai masa hari.

Asalin hoton, Getty Images
A wannan kakar an zirawa Barcelona kwallo bakwai cikin wasanni hudu da ta buga a Champions, ta yi rashin nasara a biyu, ta yi canjaras daya ta kuma ci daya.
Canjaras din da ta yi 3-3 da Inter Milan, abu ne da ya yi wa 'yan ba ruwana dadi amma bai wa kocin Barcelona Xavi dadi, saboda hakan na nufin kungiyar za ta fara shirin tafiya gasar Europa.
Wasa na gaba shi ne Clasico da Real Madrid, wanda manyan 'yan wasansu ke jin kamar sun ci Barcelona sun gama.
Idan Barcelona ta yi rashin nasara a hannun Real hakan zai janyo ce-ce-ku-ce mai yawa.
Kungiyoyin biyu ba su yi rashin nasara ba ya zuwa yanzu, amma dukkansu sun yi canjaras guda inda suka yi barin maki biyu dukkansu.










