Shekaru 10 bayan kisan gillar da aka yi wa matasa da ya gigita Najeriya

- Marubuci, By Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Port Harcourt
- An wallafa
Jane Toku ba ta zubar da hawaye ba yayin da ta ke tuna lokacin da ta ga konanniyar gawar danta a safiyar ranar da aka kona shi tare da wasu abokansa uku shekara 10 da ta wuce.
Daliban hudu sun ci karo da wasu 'yan banga ne a Aluu, wata unguwa da ke bayan Jami'ar Port Harcourt da ke yankin Neja Delta mai arzikin albarkatun mai na Najeriya.
An rika yin fashi a yankin kuma da sanyin safiyar yinin sai mutane suka zama masu zargin daliban.
Bayn an tuhume su da kasancewa barayi, sai aka yanke wa daliban hudu - Llody Toku da Ugonna Obuzor da Chiadika Biringa da kuma Tekena Elkanah - hukuncin kisa.
Nan take aka dauki mataki kansu, inda aka yi musu tsirara kuma aka rika zagaya unguwar da su ana duka, lamarin da ya kare bayan da aka cinna musu wuta da ransu, yayin da jama'a ke kallo har wasu ma na nadar bidiyon kisan da wayoyinsu na hannu.
"Da na isa wurin, sai na kutsa da karfi cikin jama'ar da suka taru sannan na tsuguna a gaban gawar dana. Na ga abokinsa Tekena na numfashi amam jim kadan bayan haka sai ya mutu," inji uwargida Toku.
Ire-iren kisan gilla irin wannan ba abakon abu ne ba a Najeriya, sai dai wannan ne karon farko da kisan ya ja hankulan miliyoyin jama'a a shafukan sada zumunta, lamarin da ya tayar da hankula da zanga-zanga a fadin kasar.
Ya kuma haifar da zazzafar muhawara kan rashin adalcin a bangaren shari'ar kasar da kuma dalilan da kan sa mutane su dauki shari'a a hannunsu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Gaskiya na gaji da zuwa nan ina kokawa kan ire-iren wadannan munanan matakan da mutane ke dauka," inji wani dan majalisar tarayya yayin da ake tattaunawa kan batun a majalisar wakilan kasar.
"Lallai ya kamata mu kawo karshen kisan gilla - mummunan abu ne," inji Yaw, wani mai gabatar da shgirye-shirye a wata tashar rediyo.
Sai dai duk da bacin rai da aka nuna da kuma yankewa wasu mutum uku tare da wani dan sanda hukunci, kan rawar da suka taka na halaka dalibai hudun, har yanzu ana daukan wannan mummunan matakin daukar doka a hannu kuma ana kashe mutane ba tare da an gurfanar da su aa gaban shari'a ba.
Daga shekarara 2019 an aikata irin wannan kisan gillar har sau 391, kamar yadda cibiyar SBM Intelligence wadda ke birnin Legas kuma ke nazari kan tashe-tashen hankula. Cibiyar ta ce a bana kawai an kashe mutum biyar ta wannan hanyar.
Wannan lamari ne da ke sa mutane su daina yarda da cewa kotunan Najeriya za su iya samo musu adalci, kamar yadda Annkio Briggs, wata mai fafutukar karae hakkin dan Adam, wadda ta jagoranci zanga-zanga a Port Harcourt kan kisan dalibai hudun domin ba za ta iya "amincewa da bangaren shari'a zai yi abin da ya dace ba," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Asalin hoton, AFP
Ba kasafai akan kama wadanda suka aikata kisan killa na taron dangi ba. Har yau ba a gurfanar da wasu mutum biyu da aka kama a watan Mayu bayan da aka kashe wata daliba Kirista saboda zargin ta yi sabo a Sokoto ba, kuma 'yan sanda sun ce ainhin wadanda suka aikata kisan sun tsere ba a san inda suka shiga ba.
Wannan na cikin kashe-kashe hudu da aka aikata a wannan watan kawai.
Na farkonsu shi ne kona wasu mutum biyu da aka yi a unguwar Ijesha ta Jihar Legas kan zargin da aka yi musu cewa sun saci wayoyin hannu.
An kuma kashe wani mutum a Lugbe, cikin yankin Abuja kan zargin wai ya aikata sabo.
Wasu 'yan acaba kuma sun kashe wani injiniya wanda ya kware wajen aiki da sauti mai suna Davida Imoh a Lekki ta Jihar Legas.
An kuma kama wadanda ake tuhuma da aikata wadannan laifukan, kamar yadda 'yan sanda ke cewa.
Amma ana iya shafe shekaru kafin a yanke musu hukunci saboda tafiyar hawainiyar da tsarin shari'ar Najeriya ke yi.
Shekaru biy da suka gabata hukumar ICPC mai binciken ayyukan cin hanci da rashawa ta ce bangaren shari'a shi ne ya fi kowanne bangaren gwmanti lalacewa a bangaren cin hanci da rashawa.
Hukumar ta ce an mika wa ma'aikatan shari'a kimanin naira biliyan tara (daidai da dala miliyan 21) a matsayin cin hanci da rashawa.

"Bai kasance marasa laifi ba amma yana da natsuwa kuma ya kasance wanda muke yin shawara tare da shi, kuma mu shaku da shi saboda mun sami danmu na biyu ne bayan shekara 11 bayan an haife shi," inji Madam Toku yayin da ta ke magana kan dan nata.
Dalibai hudun abokan juna ne wadanda shekarunsu na haihuwa na tsakanin na goma sha zuwa ashirin da 'yan kai.
Ugonna mai shekara 18 da abokinsa Lloyd mai shekara 19 - wadanda aka fi sani da sunayen Tipsy da Big L - na shirin zama mawaka ne a fagen wakar gambara a Port Harcourt.
Sai dai a karshe duk da tashin hankalin da aka tayar a sanadiyyar kisan gillar da aka yi wa wadannan matasan hudu a ba su aikata wani laifi ba, yawancin 'yan Najeriya sun juya wa batun baya.
Amma ga mahaifiya - lokaci, duk tsawonsa - ba ya dusar da rashin dan farko da ake matukar kauna wanda aka sa rai zai zama wani abu nan gaba.
"Ya kasance wanda a fagen waka zai haska sosai, wanda kawo yanz da yayi nisa," inji mahaifiyarsa Madam Toku.











