Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal da Newcastle na jiran Chelsea kan Diomande, Saudiyya na zawarcin De Bruyne
Arsenal da Newcastle United na sha'awar dan bayan Sporting Lisbon, Ousmane Diomande to amma duka kungiyoyin biyu suna jira su ga ko Chelsea za ta biya kudin da ake sa ran sayar da dan wasan na Ivory Coast mai shekara 20. (TeamTalk)
Chelsea ta bi sahun kungiyoyi da dama da ke son matashin dan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao, Nico Williams dan Sifaniya mai shekara 21. (ESPN)
Newcastle ta tattauna a kan yuwuwar sayen Pedro Neto daga Wolves a bazaran nan, a kan kudin da ya kai kusan fam miliyan 60, da ake ganin sun isa sayen dan wasan na gaba na gefe dan Portugal - kodayake Liverpool ma na sonshi. (Mail)
Tottenham ta fara tattaunawa da kyaftin dinta Son Heung-min a kan sabon kwantiragi da don Koriya ta Kudun mai sjhelkara 31, kuma tana da kwarin gwiwa kammala komai a bazara. (Football Insider)
Ita ma West Ham ta fara tattaunawa a kan dan wasan Bournemouth dan Ingila Dominic Solanke. (Football Transfers)
Arsenal, da Manchester United, da Newcastle da kuma Chelsea, dukkansu suna sha'awar sayen dan bayan Borussia Monchengladbach, dan Jamus Luca Netz, mai shekara 20. (HITC)
A shirye kungiyoyin gasar Saudiyya suke su bai wa Kevin De Bruyne, na Manchester City, sama da fam miliyan 100, domin daukar dan wasan tsakiyan na Belgium, mai shekara 32. (Football Insider)
Bayern Munich ta kara kociyan Brighton Roberto de Zerbi a cikin jerin wadanda take son dauka domin maye gurbin Thomas Tuchel a karshen kakar nan, to amma kociyan Bayer Leverkusen Xabi Alonso, wanda Liverpool, ma ke so, har yanzu shi ne kan gaba a wadanda take so. (Mirror).
Chelsean a shirye take ta karbi kudin da bai kai fam miliyan 37 ba, daga Roma, kamar yadda yake a yarjejeniyar sayen Romelu Lukaku, da ke zaman aro a kungiyar ta Italiya. (Calcio Mercato, dagaTeam Talk)
Mai yuwuwa West Ham ta nemi sayen dan wasan tsakiya na Arsenal Emile Smith Rowe, dan Ingila mai shekara 23 a bazara. (Caught Offside)
Arsenal na sa ido a kan matashin dan baya Douglas Mendes, dan Brazil mai shekara 19, wanda a yanzu yake zaman aro a Red Bull Bragantino daga Red Bull Salzburg. (Football Transfers)
Gunners da Newcastle United na sha'awar dan bayan Sporting Lisbon, Ousmane Diomande to amma duka kungiyoyin biyu suna jira su ga ko Chelsea za ta biya kudin da ake sa ran sayar da dan wasan na Ivory Coast mai shekara 20. (TeamTalk)
Dan baya Jamaal Lascelles, dan Ingila mai shekara 30, zai samu karin kwantiragi na shekara daya a Newcastle. (Chronicle)
Tattaunawa ta yi nisa tsakanin Newcastle da dan wasan tsakiya na Brazil Joelinton, mai shekara 27, a kan sabon kwantiragi. (Football Insider)