Klopp ya yabawa Nunez bayan doke Sparta Prague da ci 5-1

An wallafa

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya kururunta Darwin Nunez bayan ɗan wasan ya nuna cewa ya shirya haɗuwa da Manchester City inda ya ci ƙarin ƙwallaye biyu a gasar Europa League.

Nunez ya ci kwallayen ne a lokacin da Liverpool ta doke Sparta Prague da ci 5-1, a wasan farko a zagaye na biyu a gasar.

Dan wasan gaban na Uruguay ya zura ƙwallaye 16 a raga a kakar wasa ta bana sannan kuma ya taimaka aka zura ƙwallaye 11 duk da kalaman batanci da magoya bayan ƴan adawa ke jefa masa.

A ranar Lahadi ne Liverpool za ta karɓi baƙuncin Manchester City da kebin ta a baya a teburin Premier League da maki daya a filin wasan Anfield a wasan da ke da matukar muhimmanci ga gasar Premier League ta bana.

Nunez, mai shekaru 24, yanzu ya ci ƙwallaye biyar ke nan a wasanni huɗu idan aka haɗa da ƙwllaye biyu da ya ci a prague wanda ya sa Liverpool ta sanya ƙafa ɗaya a zagaye na gaba a gasar duk da dai za ta ƙarɓi baƙuncin Slavia rague a Anfield a mako mai zuwa.

Sakamakon sauran wasannin Europa

AS Roma 4 Brighton and Hove Albion 0

Qarabag 2 Bayer Leverkusen 2

Benfica 2 Rangers 2

Marseille 4 Villarreal 0

AC Milan 4 Slavia Prague 2

SC Frieburg 1 West Ham United 0