Wolves za ta tsawaita kwantiragin O'Neil

An wallafa

Wolves na shirin fara tattaunawa da kocin ƙungiyar Gary O'Neil kan sabuwar kwantiragi a ƙarshen kakar wasa ta bana.

An naɗa kocin mai shekaru 40 ne kwanaki biyar kacal kafin wasan farko na Wolves a Manchester United bayan Julen Lopetegui ya bar Molineux cikin ɓacin rai kan yadda ƙungiyar ke gudanar da kanta a kasuwar cinikin ƴan wasa.

Tsohon kocin Bournemouth O'Neil ya kai Wolves matsayi na 10 a kan teburi, ya kuma kai ƙungiyar zagayen daf da na kusa da na ƙarshe a gasar FA Cup.

A yanzu ƙungiyar na son tsawaita kwantiragin shekara uku da ta ƙulla da O'Neil a bazara.

Darektan wasanni na Wolves Matt Hobbs ya ce "A zahiri inda aka nufa ke nan, ya yi ƙoƙari sosai saboda haka dole mu yi wannan tattaunawar."

Ya ƙara da cewa "Na ga ana alaƙanta shi da aikin tawagar Ingila. Ya kamata sauran ƙungiyoyi su rika kallonsa.

Lokacin da muka haɗu da shi, mun yi la'akari da cewa akwai wani abu na musamman a tattare da shi."