'Yan wasan Barcelona 12 sun koma atisaye ranar Litinin

An wallafa

‘Yan wasan Barcelona 12 ne suka koma kungiyar, domin tunkarar kakar bana da za a fara a cikin watan Agusta.

Tun da sanyin safiyar Litinin ‘yan kwallon suka isa Ciutat Esportiva, inda aka auna koshin lafiyarsu.

Kungiyar kan auna koshin lafiyar ‘yan wasa domin shirin tunkarar kakar tamaula, sannan su fara karbar horo a wajen koci, Xavi Hernandez.

Cikin ‘yan wasan sun hada da R. Araujo, Sergio, Memphis, Braithwaite, Jordi Alba, Ferran da kuma, F. De Jong.

Sauran sun hada da O. Mingueza da Umtiti da Eric da Gavi da kuma Christensen.

Haka kuma matasan kungiyar 'yan kasa da shekara 19 suna daga cikin wadanda aka auna koshin lafiyarsu da suka hada da Valle da kuma Blanco.

Wasannin sada zumunta da Barcelona za ta buga:

Laraba 13 ga watan Yulin 2022

Olot da Barcelona

Laraba 20 ga watan Yulin 2022

Inter Miami da Barcelona

Lahadi 24 ga watan Yulin 2022

Real Madrid da Barcelona

Laraba 27 ga watan Yulin 2022

FC Barcelona da Juventus

Lahadi 31 ga watan Yulin 2022

New York Red Bulls da Barcelona