Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Sterling zai bar Manchester City.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
'Yan wasan Banyana-Banyana da za su kara da Burundi ranar Alhamis
Forest ta kammala daukar Williams daga Liverpool
Nottingham Forest ta amince za ta dauki dan kwallon tawagar Wales, Neco Williams kan fam miliyan 17 daga Liverpool.
Mai shekara 21 ya taimakawa Fulham ta samu tikitin shiga gasar Premier League da za a fara a bana, bayan wasannin aro da ya buga wa kungiyar daga Liverpool a Anfield.
Ya yi wa tawagar Wales gasar Euro 2020, wadda ta ssamu gurbin shiga gasar kofin duniya da a yi a Qatar a 2022.
Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin 'yan kwallo, Daga jaridu
Arsenal na da karfin gwuiwar doke Manchester United wajen dauko Youri Tielemans, dan wasan tsakiya mai shekara 25 na kungiyar Leicester da Belgium kan fam miliyan 30. (Sun)
Ita kuwa Manchester United ta taya Antony, dan wasan gaba na Brazil da kungiyar Ajax kan fam miliyan 51, sai dai Ajax ta kafe sai an ba ta fam miliyan 68 kafin ta mika shi. (Goal)
Chelsea na shirin taya Matheus Nunes, dan wasan tsakiya na Sporting Lisbon mai shekara 23 kan fam miliyan 38. Dan kasar Portugal din ya kuma ja hankalin Wolverhampton Wanderers ta Ingila. (A Bola - in Portuguese)
Chelsea za ta tsawaita kwantiragin Reece James
The i paper ta wallafa cewar Chelsea na daf da tsawaita yarjejeniyar Reece James, domin ya ci gaba da taka leda a kungiyar.
Dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 22, yana da sauran kwantiragin da zai kare a Stamford Bridge zuwa karshen kakar 2025.
Ronaldo ba na sayarwa bane - Man United
The Daily Mail ta bayar da rahoton cewar Manchester United ta jaddada cewar Cristiano Ronaldo ba na sayarwa bane duk da Chelsea da kuma Napoli na zawarcin dan kwallon tawagar Portugal..
Kwana hudu kenan Ronaldo bai yi atisayen tunkarar kakar bana ba, sai dai Mail ta ce United ta bai wa dan wasan hutu, domin ya fuskanci wasu matsaloli da suka shafi iyali.
Ko Arsenal na sson daukar Grimaldo?
The Mai ta wallafa cewar Mikel Arteta na neman, wanda zai taimakawa mai tsaron baya, Kieran Tierney.
Joe Gomez ya saka hannu don ci gaba da taka leda a Liverpool
Mai tsaron bayan Liverpool, Joe Gomez ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyar, domin ya ci gaba da taka leda a kungiyar.
Mai shekara 25, wanda ya koma Anfield a 2015, zai ci gaba da taka leda a Anfield har karshen kakar 2027.
Gomez ya yi wa Liverpool wasa 142, sai dai yana fama da jinyar rauni a gwiwar kafa da idon sawu.
Afirka ta Kudu za ta fafata da Burundi ranar Alhamis
Tawagar mata ta Afirka ta Kudu, Banyana-Banyana za ta buga wasa na biyu a gasar kofin Afirka ta mata a Morocco da Burundi ranar Alhamiss.
Afirka ta Kudu tana ta biyu a rukuni na uku, bayan da ta doke Najeriya 2-1, ita kuwa Burundi ta sha kashi da ci 4-2 a hannun Botswana.
Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin 'yan kwallo, Daga Jarida
Fulham ta ce ta yi nisa a tattaunawar da take yi da Arsenal kan golanta Leno mai shekara 30 da haihuwa. (West London Sport)
Leeds ta nemi Barcelona ta yi ma ta tayi na karshe kan Raphinha cikin wannan makon domin suna son warware dukkan sarkakiya da ta rage kan zaman dan wasan mai shekara 25 a kungiyar ko tafiyarsa zuwa wata kungiyar ba tare da bata lokaci ba. (Sport - in Spanish)
Tattakin da Super Falcons ta yi ranar Alhamis
Tattakin da tawagar mata ta Najeriya da ta yi ranar Alhamis, kafin wasa na biyu a rukuni na uku da za ta yi da Botswana a gasar cin kofin Afirka a kwallon mata a Morocco.
Barcelona za ta fara sayar da tikitin kallon wasan Gamper Trophy
Ranar Juma'a Barcelona za ta fara sayar da tikitin kallon wasan Gamper Trophy na 2022 da za a yi a Camp Nou.
Barcelona za ta fafata da Pumas ranar 7 ga watan Agusta da kungiyar da ake kira Club Universidad Nacional ta México, wadda ake kira Pumas..
Haka kuma Barcelona za ta fara sayar da tikitin kallon wasan matan kungiyar da za ta yi da Montpellieron ta Faransa ranar Talata 23 ga watan Agusta.
Chelsea ta shiga zawarcin Frenkie de Jong
Corberan ya bar aikin kocin Huddersfield
Leicester City ta dauki Josie Green
Leicester ta dauki 'yar kwallon tawagar Wales, Josie Green mai shekara 27, wadda ta bar Tottenham bayan kammala kakar da ta wuce.
Bajintar Sterling a Manchester City
Raheem Sterling ya lashe kofin Premier League hudu da FA Cup da kuma League Cup hudu a kaka bakwai da ya yi a Manchester City.
Mai shekara 27 na daf da komawa Chelsea a bana, duk da saura kaka daya yarjejeniyarsa ta karkare a Etihad.
Shin ta yaya za a ke tuna Sterling a Manchester City.
Shin ko Manchester United za ta dauki Antony kuwa?
Jaridar Mirror ta wallafa cewar tayin da Manchester United ta yi wa Anthony, Ajax ta ce kudin ko kusa bai kai yadda za ta sallama dan kwallon ba.
Afirka ta Kudu na murnar shekara 30 da komawa buga tamaula
Ranar Alhamis Afirka ta Kudu ke bikin cika shekara 30 da kasar ta koma buga tamaula tsakaninta da kasashe, bayan da aka kawo karshen mulkin mallaka.
Sai dai ranar uku ga watan Yulin 1992 aka mayar da Afirka ta Kudu cikin mambobin hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, wadda ta dakatar da ita a 1964.