Arsenal za ta ɗauki Osimhen, Napoli na zawarcin Lukaku

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta ci gaba da zawarcin ɗan wasan gaban Napoli da Najeriya mai shekara 25, Victor Osimhen. (Corriere dello Sport - in Italian)

Napoli na nazarin yadda za ta ɗauki ɗan wasan gaban Belgium da Chelsea mai shekara 31, Romelu Lukaku, a wata yarjejeniya da za ta iya kaiwa ga musayan ɗan wasan da Victor Osimhen. (Guardian)

Ɗan wasan bayan jamhuriyar Ireland mai shekara 23, Jake O'Brien, ya isa Merseyside domin duba lafiyar sa da kuma kammala ƙulla kwangilar £17m da za ta ba shi damar sauya sheƙa daga Lyon zuwa Everton. (Guardian)

Everton za ta gabatar da tayin ɗan wasan tsakiyar Strasbourg da Senegal mai shekara 20, Habib Diarra. (L'Equipe - in French)

Ƙungiyoyin Turai da dama sun nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gefen Luton mai shekara 24, Tahith Chong, a kan kuɗi £10m. (Sky Germany)

West Ham za ta gabatar da tayin ɗan wasan tsakiyar Faransa da Monaco mai shekara 25, Youssouf Fofana, amma rahotanni na cewa ɗan wasan ya fi sha'awar komawa AC Milan.(Givemesport)

Tsohon mai tsaron ragar Manchester United mai shekara 33, David de Gea ba zai koma Genoa ba, kuma babu wata jarjejeniya tsakanin ɗan wasan Sifaniyan da kungiyar Italiyan. (Fabrizio Romano)

Arsenal ta bayyana sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Jamus da Bayern Munich mai shekara 28, Leroy Sane amma da wuya ɗan wasan ya iya sauya sheƙa a bana (Sky Germany)

Har yanzu Tottenham ba ta ƙulla wata yarjejeniya ba domin sallama ɗan wasanta ɗan Brazil mai shekara 25, Emerson Royal AC Milan.(Ben Jacobs)

Ɗan wasan gaban Villarreal da Chile mai shekara 25, Ben Brereton Diaz, ya isa Southampton domin duba lafiyarsa, gabanin komawar sa ƙungiyar gasar firimiyan (Football Insider)