Fulham ta ɗauki Smith Rowe daga Arsenal

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Fulham ta cimma yarjejeniya da Arsenal don sayen, Emile Smith Rowe kan fan miliyan 27 da cewar za a yi karin fan miliyan 7 na tsarabe-tsarabe.

Smith Rowe shi ne wanda aka ɗauka mafi tsada a Fulham kuma majiyoyi sun karin tsarabe-tsaraben ya ƙunshi nasarar da Fulham za ta yi a kofuna da samun shiga gasar zakarun Turai.

Dan wasan mai shekaru 23, zai bar Arsenal, bayan kaka biyu da ya yi a babbar ƙungiyar da zarar an kammala ƙulla yarjejeniyar.

Smith Rowe ya fara daga makarantar koyon tamaula ta Gunners har zuwa babbar ƙungiyar daga baya aka daina amfani da shi sabo da ƙwazon Gabriel Martinelli da Leandro Trossard da kuma Bukayo Saka.

Ɗan wasan ya buga wa tawagar Ingila wasa uku, kuma na karshe da ya yi mata shi ne a shekarar 2022.

A halin da ake ciki, Arsenal ta sayi ɗan wasan bayan tawagar Italiya, Riccardo Calafiori daga Bologna kan fan miliyan 42.