Arsenal ta kammala ɗaukar Calafiori daga Bologna

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta sayi ɗan wasan bayan tawagar Italiya, Riccardo Calafiori daga Bologna kan fan miliyan 42 ciki har da tsarabe-tsarabe.

Ɗan wasan mai shekaru 22, wanda ya buga wasa uku a cikin rukuni a gasar nahiyar Turai a Euro 2024, ya kulla yarjejeniyar shekara biyar da Gunners.

Nan take yana tare da ƴan wasan Arsenal da ke buga wasannin sada zumunta, domin tunkarar kakar bana da take yi a Philadelphia.

Calafiori na iya taka leda a matsayin mai tsaron baya daga tsakiya ko kuma daga gefen dama - wanda a baya ya buga gaba daga gefen dama.

Ya buga wa Bologna wasa 30 a gasar Seria A ta bara, inda ya ci kwallo biyu ya kuma bayar da biyar aka zura a raga.

Bologna ta kare a mataki na biyar a teburin Serie A kakar da ta wuce da samun gurbin Champions League da za a buga a bana.

"Muna maraba da Riccardo da iyalinsa zuwa Arsenal," in ji Arteta. "Shi babban ɗan wasa ne, kuma zai bamu damar karfafa gurbin masu tasre bayanmu.

"Muna fatan yin aiki tare da Riccardo da burin zai taka rawar gani a Gunners, sannan za mu more shi har zuwa zaman da zai yi a ƙungiyar.''