Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Messi ya ci kwallo na 700 a lik, Mpappe ya zura na 200 a PSG
Lionel Messi ya ci kwallo na 700 a lik, Kylian Mbappe ya zura na 200 a Paris St Germain a wasan da ta ci Marseille ranar Lahadi.
PSG ta je ta doke Marseille 3-0 a wasan mako na 25 a Ligue 1, inda Kylian Mbappe ya ci biyu, Messi ya zura daya a raga.
Kyaftin din tawagar Argentina ya zama na biyu - bayan Cristiano Ronaldo da ya zazzaga kwallaye da yawa a raga a manyan gasar Turai biyar.
Kylian Mbappe ne ya ci biyu a karawar ta Ligue 1, ya kuma yi kan-kan-kan da Edinson Cavani, wanda ya ci wa PSG kwallo 200.
Da wannan sakamakon PSG ta ci gaba da jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Faransa ta zarar maki takwas.
Mbappe mai shekara 24 ya ci kwallo 200 kasa da wasa 250, tun bayan da ya koma kungiyar daga Monaco a 2017.
Kawo yanzu Messi, wanda ya lashe kofin duniya a Qatar tare da Argentina ya ci kwallo 28 a PSG, tun bayan da ya koma kungiyar a Disambar 2021 daga Barcelona.
Ya ci kwallo 672 a wasa 778 a Barcelona, kungiyar da ya fara yi wa tamaula tun yana da shekara 13 da haihuwa.
Ya lashe Ballon d'Or bakwai da daukar kofi 35 a Barcelona da karin wasu biyu a PSG.
Ana sa ran Messi, mai shekara 35, shine zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa na 2022, wato Fifa Best award da za a yi bikin ranar Litinin.
Tun a farkon kakar nan Ronaldo ya haura cin kwallo sama da 700 tun yana Manchester United, wanda ya koma Al Nassr ta Saudi Arabia da cin kwallo 701 a Turai.
Messi, wanda ya ci kwallo 98 a tawagar Argenyina, na daf da zama na uku da suka ci wa kasar kwallo 100 a tarihi.