Arteta ya ce hakkinsa ne ya kare Arsenal

An wallafa

Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce "ya zama wajibi" ya kare kulob din bayan ya caccaki alkalin wasa a karawar da Newcastle ta doke su da ci 1-0 a ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce shawarar da aka yanke kan kwallon Anthony Gordon a St James' Park "abin kunya ne" kuma "abin takaici".

Arsenal ta goyi bayan kalaman Arteta a wata sanarwa da kungiyar ta fitar, wadda tsohon dan wasan Manchester United Gary Neville ya kira abu "mai hadari".

"Ya zama wajibi gare ni in tsaya a gabanku in bayyana gaskiya ," in ji Arteta a ranar Talata.

"Aikina shi ne kare 'yan wasana da kuma kulob dina ta hanya mafi kyau, abin da nake da niyyar yi ke nan a kowanne lokaci.''

Rashin nasara a Newcastle ya kawo karshen wasan da Arsenal ta yi a gasar Firimiya ba tare da an doke ta ba, abin da ya sa ta zama ta hudu, inda akwai maki uku tsakaninta da Manchester City da ke jan ragamar teburin.

A ranar Laraba ne Gunners za ta karbi bakuncin Sevilla a gasar zakarun Turai a rukunin B.